Gwamna Matawalle ya sanya hannu a yarjejeniyar samar da zaman lafiya, tare da Gwamnonin Katsina, Sokoto, da Hajar Maradi.

Mai Daraja gwamnan jahar Zamfara,Hon Dr. Bello Mohammed MON (Matawallen Maradun) ya Sanya hannu a yarjejeniyar Samar da zaman lafiya tare da takwarorinsa gwamnonin Katsina, Sokoto da Maradi.

Yarjejeniya wadda ta wakana Fadar Gwamnatin jahar Maradi ta janhuriyar Niger bayan kammala wani taro kan matsalar tsaron Iyakar Zamfara, Sokoto, Katsina da Gwamnonin jahohin su ka yi a Maradin ta janhuriyar Niger.

Wannan taron dai gwamnan jahar Maradi Mallam Zakari Umaru ne ya shirya shi domin hada Kai ta yadda za a samu bakin zaren magance matsalar tsaron da ake addabar Iyakar kasashen biyu.

Yarjejeniyar dai ta kunshi, yadda jahohin uku na Nigeria ta su Kara zage damtse domin magance matsalar ‘yan bindiga da ke dabbar jahohin da ke da iyaka da kasar Niger din.

Wasu daga cikin Abubuwan da aka tattaunawa su ne hada hannu da jahohin da ke fama da matsalar ‘yan bindiga, masu satar Shanu, masu satar mutane da kuma ‘yan fashi da Makami domin samun da zaman lafiya a jahohin.

Yarjejeniyar ta kunshi hada kwamitin da zai tsara yadda za yi aiki na keke-da-keke domin Samar zaman lafiya a jahohin da matsalar ke addaba.

Tun farko da ya ke Jawabi a wajen taron, gwamna Matawallen Maradun, ya bayyana cewa muddun ana son a samu zaman lafiya a jahohin, to dole a rungumi tattaunawa tare da Hawa kan teburin sulhu shi ne kurrum zai kawo karshen matsalar tsaron.

Ya kuma Kara da cewa, lokacin da Gwamnatinsa ta zo hanyar sulhu ta bullo da ita tare da tuntubar bangarorin ‘yan bindigar Wanda ya sa dukkanin bangarorin suka yarda aka zauna teburin Sulhu. Wanda zaman sulhun ne ya haifar da zaman lafiya a jaharsa.

Gwamnan dai ya halarci taron ne da dukkanin shuwagabannin bangarorin hukumomin tsaro na jahar Zamfara. Wadanda su ka hada da ‘yan sanda, jami”an tsaron ciki, da kuma na fararen kaya.

Gwamnonin Katsina da Sokoto, Rt.Hon.Aminu Bello Masari da Rt.Hon.Aminu Waziri Tambuwal su ma sun zo da ta su tawagar a wajen taron.

Yusuf Idris GUSAU
Babban Daraktan Watsa Labarai a fadar Gwamnatin jahar Zamfara.
Fassara: Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau.

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment