Gwamna matawalle ya bayar da umarnin a biya malamai 556. Da Gwamnatin AA yari ta dauka aiki, ta kasa biyansu albashi

Mai Daraja gwamnan jahar Zamfara Hon Dr. Bello Mohammed MON (Matawallen Maradun, Barden Hausa) ya bayar da umurnin a ɗauki Malamai 556 da tsohowar Gwamnatin da wuce ta ɗauka aiki, Amma ta ƙi biyansu albashi da sauran haƙƙoƙinsu.

Gwamnan ya bayyar da wannan umurnin ne ga shugaban ma’aikatan jahar Zamfara. Alh. Kabir Balarabe Sardaunan Ɗan’isa. Inda ya murce shi da ya tabbatar an Fara biyansu albashi tun daga wannan watan na satumba .
Matawallen ya yaba da haƙurinsu. Haka zalika ya roƙe su da su zama masu ɗa’a ga dokokin aikin Gwamnatin.
Mayar da waɗannan matasa yana ɗaya daga cikin gudurin Gwamnatin Matawalle na sauraren koken Al’umma masu ma’ana da za su taimaka wajen haɓɓakar cigaban jahar Zamfara.
Waɗannan Malamai 556 dai sun tare gwamnan ne a ranar Litinin ɗin da ta gabata Inda su ka koka masa, akan halin da su ke ciki lokacin da ya zo gidan Rediyon jahar Zamfara domin yin shirin “Zuwa da kai” Inda nan take ya bayar da umurnin shugaban ma’aikatan ya saurari koken malaman tare da kawo masa rahotonsu, bayan ya kammala bitarsa.
Bayan shugaban ma’aikatan ya saurari malaman ya tabbatarwa gwamnan tabbas koken Malaman na Gaskiya ne. Dan haka Nan take ya bayar da umurnin a maida su kan aikinsu, da gaugawa.
Idan dai ba a manta ba, ko a watan da ya shuɗe Gwamnatin Matawallen ta dawo da ma’aikata 1040 cikin 1400 da Gwamnatin da ta shude ta Abdul’azizu Yari ta ɗauka aiki shekaru biyar ba ta biya su albashi ba. Wanda har ya cilasta su Kai Gwamnatin jahar Kotu. Domin Nema masu haƙƙoƙinsu. Wanda tuni wannan gwamnatin ta fara biyansu albashi.

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment