GUNGUN ‘YAN BINDIGA SUN MIKA WUYA GA GWAMNATIN ZAMFARA

A jiya jumu’a 30-8-2019 wasu gungun ‘yan bindiga da su zama ɗaya daga cikin waɗanda ba su Miƙa wuya ga shirin sulhun Gwamnatin jahar Zamfara ba. Cikin ikon Allah yau sun Miƙa wuya.

Da ya ke Jawabi shugaban ‘yan bindigar da ya tuba yau ya kuma Miƙa wuya ga shirin sulhun ABU GALA Wanda kwamandan wani kwamanda ne a Ɗansadau da ke ƙaramar hukumar Maru. Ya bayyana cewa; ” Mun Mika wuya ne, domin ganin yadda Gwamnatin Matawallen Maradun ta ɗauki wannan shirin da Gaskiya, kuma mun ga yadda ake ƙoƙarin ganin cewa wannan Gwamnatin na aiki tuƙuru domin Samar da zaman lafiya kuma mun ga Don Allah Gwamnatin ke yi. Wanda Hakan ne ya sa yau na kwaso jama’a ta domin mu Miƙa wuya kamar yadda ku ka gani. Domin haka za mu yi duk iya ƙoƙarinmu domin tallafawa wannan Gwamnatin. Domin samun nasararta.

Da ya ke Jawabi Mai Daraja gwamnan jahar Zamfara Dr Bello Mohammed Matawallen Maradun, ya nuna jin ɗaɗinsa matuƙa gaya ga wannan miƙa wuyan da waɗannan Tsofaffin ‘yan bindiga su ka yi. Kuma ya yi masu alƙawarin aiki tuƙuru domin tallafawa rayuwarsu kamar yadda ya Fara. Domin inganta rayuwar al’ummar karkara, ta fuskoki da dama domin samun cigaban rayuwar Fulanin.

Haka zalika gwamnan ya yi, Kira ga Tsofaffin ‘yan bindigar da su yi ƙoƙarin Ganin sun Miƙa makamansu a Hannun Gwamnatin jahar Zamfara wadda za ta Mika su ga jami”an tsaro.

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

One thought on “GUNGUN ‘YAN BINDIGA SUN MIKA WUYA GA GWAMNATIN ZAMFARA

Leave a comment