Gwamnan Zamfara zaizo ma Zamfarawa da gagarumin albishiri.

Gwamnan Jahar Zamfara Hon (Dr) Bello Muhammad (Matawallen Maradun) zai shigo da gagarumin tallafin bankin raya kasashen Africa. Domin zuba jari a fanonni da dama domin ya ye talauci da farfado da tattalin arzikin Jahar Zamfara.


A ranar talatan nan mai zuwa dai ne ake saran dawowar gwamnan a Jaharsa, inda ya kwashe sama da kwanaki (10) a birnin tarayya Abuja domin kawo karshen matsalolin Jahar Zamfara.

Mai daraja Gwamnan Jahar Zamfara ya yi wadan nan kwanakin ne domin kai karshen yarjejeniya da bankin raya kasashen Africa.

Gwamnatin Jahar Zamfara ta kulla yarjejeniya da bankin raya kasashen Africa na kawo daukin kudi dala biliyan daya, inda da wadan nan kudi za’a yi aiki da Su a bangaren gina filin jirgin sama, da gyara layin dogo, harkar noman auduga, gyara masakun Jahar Zamfara tare da gina kwata ta zamani wacce za’a iya yanka shanu a tura naman daga Zamfara zuwa kasashen ketare.

Sannan Gwamnan Jahar Zamfara ya samu tallafi daga mai girma shugaban kasa Muhammad Buhari inda ya bada tallafin tilera Hamsin ta takin zamani tare da irin masara, gero, da sauransu domin tallafawa mutanen da iftila’in matsalar tsaron Jahar Zamfara ya ‘dai-‘daita.

Haka zalika Mai daraja gwamnan Jahar Zamfara zaizo da tawaga ta musamman wanda zasu duba illar da Jahar Zamfara ta samu na kashe kashen ‘yan bindiga domin taimakawa wadan da wannan tashin hankali ya raba da gidajen su da dukiyoyin su.

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment