Wasu kadan daga cikin falalar ranar juma’a.

Juma‘a ita ce mafi girma a cikin ranaku da ALLAH Madaukakin Sarki ya halitta, ta yadda ya bawa yahudawa zabi sai suka zabi asabar, sa‘annan Ya bawa nasara zabi sai suka zabi lahadi, mu kuma al‘ummar Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallam sai ALLAH ya azurta mu da wannan rana ta juma‘a.

A cikin tane ALLAH Madaukakin Sarki ya halicci babanmu Annabi ADAM (AS) kuma a cikin wannan rana aka sauko da shi daga AL-JANNAH, kuma a cikin irin wannan rana ALLAH Madaukakin Sarki zai tashi alqiyama.

Hadisi ya tabbata a cikin muslim cewa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam yace idan ranar juma‘a ta zo duk halittun ALLAH Madaukakin Sarki hankalinsu a tashe yake (sabo da tsoran kada ALLAH ya tashi qiyama a wannan ranar). Sai mutum da al-janni kawai hankalin su yake a kwance.

Haka kuma yana daga falalar ta juma‘a Manzon ALLAH Sallallahu Alaihi Wasallam yace akwai wata sa‘a wanda duk ya risketa yana mai addu‘a to ALLAH zai karbi addu‘arsa. Muslim ne yarawaito.
Ana son kamewa da yawaita zikiri da salatin Annabi da iyalan gidansa (a.s). Ana son
yawaita karatun al-qur’ani da addu’o’i ko sauraransu ta hanyar radio.

Yana daga cikin sunnar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam yana karanta suratul KAHFI kowacce juma‘a. Da dai sauran falalar ta masu dinbin yawa.
Ya dan uwa ka kasance mai koyi ga abubuwan shugabanmu Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallam.

Ya ku musulmi! mu yi gasa a kan wannan alheri mai girma, wanda Allah ya sanya shi cikin ranar Juma’a ga wanda ya sunnanta da sunnan Annabi a cikin wannan, mu tsaftacce jukkunanku, mu sanya mafi kyawun tufafin mu, mu yi asuwaki, mu sanya turare, mu yi sammako don mu tafi sallar Juma’a, mu lazimci ladubban Annabi (S.A.W), da tsari na Muhammadiyya. mu kasance daga masu rigaye zuwa alherai, masu rabauta da mafiya daukakar darajoji.

(Wannan falala ce ta Allah da yake ba da ita ga wanda yaso, kuma Allah shi ne ma’abocin falala mai girma).
Allah ya bamu albarkacin wannan rana. Ameen

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment