Gwamnatin jahar Zamfara za ta samawa matasa dubu biyu aikin yi a karkashin Hukumar Rage Cinkoson Ababen Hawa akan Hayoyin Jahar, mai suna ZAMFARA STATE ROAD TRAFIC AGENCY (ZAROTA).
Sabon kwamandan hukumar na jahar Alhaji Aliyu Alhazzai Shinkafi ya sanar da hakan, a zantawarshi da manema labarai a garin Gusau dake cikin jahar Zamfara.
Alhaji Aliyu Alhazzai ya bayyana cewa matasa dubu biyu da Hukumar za ta dauka aiki, kari ne a kan daruruwan matasan da suka dauki dogon lokaci suna bautawa al’umar Jahar a karkashin wannan hukuma ta ZAROTA a cikin jahar.
Kwamandan hukumar ya yi bayanin cewa, za a soma biyan dukkanin matasan da hukumar ta dauka aiki, domin samun nasarar kawar da zaman kashe wando da ya yi wa wasu matasan jahar katutu a wannan lokacin.
Da ya juya a kan dangantakar hukumar ZAROTA da sauran hukumomin tsaro dake aiki a cikin Jahar, Alhaji Shinkafi ya ce,Hukumar ZAROTA tare da Hadin Gwiwar sauran Hukumomin Tsaro, za su dauki matakin kawar da cinkaso da ake fuskanta a wasu manyan garuruwa na jahar ta hanyar gudanar da kasuwanci akan hanyar mota.