Da Sunan Allah, Salati da Sallama su tabbata ga Manzo da Iyalansa da Sahabbai.
Daga: Sheak Abdulhakeem Ahmad Ya’akub Gusau.
Kasancer aikin Hajji, ba rana daya akeyinsa ba
Don haka zanyi bayanin dai dai da ranakun aikin:
RANAR 8, GA WATA
Ana fara aikin Hajji ne, ranar takwas ga watan Zulhajj, ana karanta (Yaumu Tarwiyati)
A wannan rana mai Hajjin Tamattu’i, zai daura Harma da Hajji da Hantsi
1. Zaiyi wanka, da duk abinda yayi lokacin Umra
Na gusar da gashi, cire kumba, daura Harami da sauran su
2. Zai yi niyya da Hajji, kamar yadda lokacin Umra, illah a wannan Niyar Hajji zai yi
Zai CE: Labbaika Hajjan, bayan kuma yayi Niya a zuciya
Ko Nawaitul Hajja Wa’ahramtu bihi lillahi Ta’alah
Idan yakara da: Rabbana Taqabbal miniy ba komi
3. Daga za’kawo motoci a daukeku zuwan filin Mina
Za’atafi ne, ana Talbiya(Labbaikallahumma Labbaik…)
4. An so zuwa filin Mina kafin rana ta karkata,(Zawwal)
Idan an sa6a dai ba komi, amma dai a yawaita Talbiya
5. Za’ayi Sallolin Azuhur da La’asar da Magrib da Isha’i
Sai dai Azuhur da La’asar da Isha’i kowace raka’a 2, amma a lokacin ta
6. Za’a kwana anan har gari ya waye, rana ta fito, sai a tasamma arafa
RANAR 9, GA WATA, WUNIN ARFA
A Wannan rana ne, ake tsayuwar Arfa
1. Za’a tafi ana Talbiya har a isa a cikin filin Arfa
Idan akaje Arfa, anso a sauka Namira, idan yayiwu, inbai samuba duk Inda ka tsaya yayi
Sai dai wurinda ake kira da (Badni Uranata) ba’atsuya nan
2. Idan rana ta karkata (Zawwal)
za’ayi Sallolin Azuhur da La’asar tare
Za’ayi su a jam’i, kowace raka’a 2, kiran Sallah 1, ikama 2
Anso a saurari Khuduba daga Limamin arfa, don jin hukunce hukuncen Hajj
Daga nan tsayuwar Arfa zata fara, har faduwar rana
3. Tsayuwar Arfa, na nufin kasancewar Alhaji a filin Arfa, ana addua da zikrori
Daga karkatawar rana zuwa faduwarta, a tsaye ko zaune koma kwance
Koda mutum baya lafiya, yazo filin yazauna koda baisan ankawo shi ba, tsayuwarsa tayi
Ko rana ta fadi, mutum bai zo Arfa ba, bata kubce masa sai alfijir ya hudo
Ana son yawaita addua fiyeda ko’ina, da tuba da kuka da kastastarda kai ga Allah
Yazo a Hadisi, yana cikin mafi girma Zunubi mutum yayi tsayuwar
Arfa yayi tunanin ba’a Gafarta masa.
Mafi girman abinda Annabi saw ya fada da sauran Annabawa bayan addua, shine
La’ilaha lllallahu wahdahu lasharika lahu lahul mulku, walahul hamdu wahuwa alah kulli sha’in, Qadirun
Kuma anfi so Alhaji kar yayi Azumi, don jin kafin tsayuwar arfa, ba za’ayi Magri da Isha’a filin arfa ba.
ZUWA MUZDALIFA:
1.Bayan faduwar rana ana filin Arfa, da sharadin a tabbata ta fadin
Daga nan, sai a tasarwa filin Musdalifa cikin cikar nazuwa, ba ture_ture
Amma yanzu dayake ana daukar Alhazai ne da motoci, to sai su Kira
Koda andade ba’a kawo mota ba, ko andade ba’a kwashe kuba ba komi
2. Ba za’ayi Sallolin Magriba da Isha’i, ba sai can koda lokaci yatafi
3. Abubuwan da zakayi a filin Muzdalifa:
Ya tabbata ya shiga cikin filin Arfa, kafin ya ajiye kayansa, akwai alamomi
*A fara yin Salloli kafin komi, dazarar an isa
Kuma za’ayi Magriba raka’a 3, Isha’i raka’a 2, Jam’i lokaci 1, kiran Sallah 1, Iqama 2
* Ya nemi abinci yaci idan yana bukatar haka
* Ya kwanta da wuri yayi bacci, don aikin dake gabansa gobe
Wajen baccin ba’arufe kai, kuma kar a shagaltu da fira, ko tsintar duwatsun jifa
4. Idan Asuba tayi sai ayi Sallar Asuba, cikin Jam’i, kuma sai a zauna gari ya waye
5. A nan ne, Allah yayi horo ayita zikirin Allah, a Mash’airl Haram, yanzu Masallaci ne
Za’a tsaya wajen ayita zikiri har sai rana tayi kusa 6ullowa, ana addua tareda daga hannuwa
Sai a bar filin kafin fitowar rana zuwa Mina don jifa.