Za mu hada hannu da manyan ma’aikatu wajen zakulo wadan da ake zargi

Shugaban Hukumar Korafe-Korafe da yaki da Almundahana ta kasa Reshen Jihar Kano Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado, ya Ce za su Hada Hannu Kanana da Manyan Ma’aikatun Gwamnati wajen Zakulo wadanda ake zargi da yin Almundahana da Dukiyar Jama’a.

Daga; Mu’azzam Yakubu Sanka

Rimin Gado, ya cigaba da cewa domin ganin ana Sarrafa Dukiyar Al’umma yadda ya kamata dole sai mun hada hannu da dukkan wani bangare na Ma’aikatun Gwamnati da Masu Zaman Kansu saboda Kwalliya ta biya Kudin Sabulu, Inji shi.

Barista, ya ce Muddin Jama’a za su Ba mu Goyon Bayan da Muke Bukata Tabbass Batun Cin Hanci da Rashawa zai zama Tarihi a Kasar nan.

Muhuyi, ya ce duk da dai mun San akwai Wadanda suke da Bayanan da za su ba mu amma suna gudun kada wani abu ya samesu ko kuma wani tsoro na daban muna tabbatar musu cewa su Dogara ga Allah domin Yaki da Rashawa tamkar wani Jihadi ne, inji shi.

Ya Kara da cewa mune ‘yan Najeriya Dan haka tilas mu zamu kawo sauyi Mai ma’ana a cikinta domin babu Wanda zai shigo daga waje ya gyara maka gidan ka Alhali Kai kana zaune dole sai ka mike kayi wani Kazar-kazar kafin kayi Nasara, inji shi.

A wani Bangare kuma Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da yi ma Tattalin Arziki zagon Kasa Ibrahim Magu, ya Yabawa Barista Muhuyi Magaji, da Kokarin da ya ke yi Wajen Tsaftace Jihar Kano, da Kasa Baki daya.

Ya kuke Kallon wannan Yunkurin?

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment