Shirin ruga yana nan daram za’a aiwatar a Jahar Zamfara.

Gwamnatin Zamfara za ta aiwatar da shirin rugga domin kawo karshen matsalar tsaron Jahar.

Mai daraja gwamnan jahar Zamfara ya yi zama na musamman da masu ruwa-da-tsakin daga bangaren ‘yan bindiga, shuwagabannin Fulani, ‘Yan sa-kai. A cigaba da yunkurin gwamnan na Samar da tsaro ta hanyar sulhu a jahar Zamfara.


Tun da farko dai shuwagabannin duka bangarorin sun yi Jawabai akan farkon matsalar Da abunda ya sa su yinta. Tare da bayyana cewa, dukkaninsu sun shiga sha’anin ta’adanci ne, Domin zalunci ta bagarori Da dama. Inda sun ka bayyana jin dadinsu matuka gaya ga yunkurin gwamnatin inda su ka yi Alkawarin cewa za su yi iya yinsu Domin tallafawa yunkurin na Samar da tsaro.

Da ya ke maida jawabi Mai daraja gwamnan jahar Zamfara Hon Dr Bello Mohammed (Matawallen Maradun) Ya bayyana cewa Gwamnatinsa babban shirinta shi ne kawo Karshen matsalar tsaron jahar Zamfara.

Gwamnan ya bayyana cewa;

” Hakika akwai wata boyayyar manufa da wasu Da ba su kaunar Fulani su ke Da ita. Domin Ana yin haka domin a hana al’ummarku shiga Al’umma Kwata-kwata, Dan haka duk Wanda zai zo maku Da labarin cewa, maganar zama lafiya karya ce, to ka da kadda ku yarda da su Domin wallahi ba masu sonku ba ne. Misali ku ne ku ke zuwa ku sato shanu, san da yana naira dubu dari biyu Amma ya ba ku naira dubu goma ko ashirin, Amma shi ya na gida yana shan ac Amma ku rayuwarku a cikin daji kusan a walakance ba.

“Dan haka gwamnatina ta na cigaba da shirye-shirye Domin tallafawa rayuwar al’ummar jahar Zamfara Saboda haka Na yi alkawarin cewa zan gina maku ruggage uku a jahar Zamfara. Za mu sama maku, makarantannin Boko, na Arabiya Assibitoci da kuma sauran kayan masarufi. Haka zalika za mu kawo maku Wata ciyawa Wadda za ta Taimakawa dabbobinku rani da damina. Duk wadannan shirye-shiryen zan yi su ne,da dukiyar al’ummar jahar Zamfara

“Za mu zabi dattijai daga cikinku domin Za mu rinka Mika masu ragamar jagorancin al’ummarku, haka zalika Zamu yanka maku albashi, domin ba za ba za mu so a wayi gari mutanenmu na shigowa dauke ma miyagun makamai, suna kisan junansu ba, bukatarmu ku samu ilimi ba bindiga ba. Duk Wanda bai samu ilimi ba, ba zai iya zama wani ba. Mu nan da ku ke ganinmu ribar ilimin mu ke ci. Saboda haka ina kira gare ku iyaye da ku fadiwa yaranku shirinmu shi ne, mu Samar maku Da ilimi da hanyoyin dogaro da Kai.

Haka zalika Shi ya ina neman ARZIKI babbar SALLAH ina son a yi wasan sharu kamar yadda aka Saba, Domin Samar da hadin Kai. Kamar yadda ku ka sani mun bude kasuwanni kowa ya zo ya ci kasuwa.

Kuma insha Allahu, Na yi maku alkawarin duk yaranku Da ke hannun jam’an tsaro za a sake su, kamar yadda na yiwa HUSAINI jiya-jiya aka sanar da ni cewa an kama shi, yau ga shi tare da ku

Muna da shiri mai kyau, Amma ba mu iya aiwatar shi sai mun hada Kai, da ku Kuma Da shuwagabannin dabobi ne za su jagoranci yankinsa.

Ga shugaba Buhari ya mu Zamfara mu kai karshe za mu RI rugga. Za mu yi wanan runggar da kudin al’ummar jahar Zamfara. Daga yau zuwa litinin za a Fara aiwatar da shirin Rugga. Kuma duk wani informa ko Mai garkuwa mutane da, Dan banga, in an Kama shi hukuncinsa shi ne kisa.

Dan haka insha Allahu Dukkanin gwamnonin Zamfara, Sokoto, Kebbi, katsina da Nigeria, zan zauna Da su Domin fadi masu na daukar masu alkawari. Cewa ta hanyar sulhu ne, za mu kawo karshen matsalar.

Zaman dai ya samu halartar Gwamnan jahar Zamfara Hon Dr Bello Mohammed Matawallen Maradun, mataimakin gwamnan jahar Zamfara Batista Mahdi Aliyu Gusau, Mataimakin gwamnan jahar Sokoto, Mannir Dan’iya, Sakataren gwamnatin jahar Zamfara, Bala Bello Maru, Kwamishinan yan SANDA na jahar Zamfara Sarakunan Zurmi da GUMMI, Mai baiwa gwamna shawara ta musamman a bangaren tsaro da kuma shugaban kungiyar Fulani ta kasa. Da sauran Muhimman Mutane daga bangarorin masu ruwa Da tsakin duka

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment