Matawalle ya kama hanyar magance matsalolin matasan Jahar Zamfara.

His Excellency Dr.Bello Muhammad Matawalle Ya Kama hanyar Magance Matsalolin Matasan Jahar Zamfara.


Matsalar rashin aikinyi a tsakankanin matasa tana daya daga cikin ummul khabi’isar kowanne irin komawa baya a cikin al-umma wanda rashin ayyukanyi ya haddasar da fitintinu kala daban daban a cikin jahar Zamfara amma Allah cikin ikonsa His Excellency Bello Matawallen Maradun ya kama hanyar magance wadannan matsalolin.

Bayan shafe shekaru takwas da gwamnati Abdul-Aziz yari tayi ba tare da daukar kowanne matashi aiki ba hasalima ma ta kori ma’aikata akalla dubu goma tare da cewa ta dauki wasu dubu daya da dari hudu (1,400) ba tare da biyansu albashi ba har tsawon watanni sittin inda daga karshe ma gwamnatin tayi fatali da daukan su aiki da akayi.

A cikin watanni biyu na Zuwan His excellency Gov.Matawallen Maradun ya shirya tsaf domin magance zaman banza a tsakankanin Matasa inda yayi abubuwa kamar haka.

1-Mayarda Ma’aikata dubu daya da dari hudu (1400) da aka dauka ba tare da an biyasu ba tsawon watanni sittin tare da biyan albashinsu nan take.

2) Dawoda Hukumar kiyaye hadurra da kula da zirga zirgar ababen hawa (Zarota) wacce keda matasa fiye da dubu goma wadanda suma tsohon gwamna yayi fatali da su.

3- Kirkiro Hukumar ZASIP wacce zata dauki matasa dubu hudu aiki domin rabasu da zaman kashe wando.

Tabbas mun shaida mun amince Bello Matawalle masoyin Zamfarawa ne inada yakinin a cikin shekaru hudunsa na farko Jahar Zamfara zata kere sa’o’inta takowanne fanni.

Mu dage da yiwa mai girma gwamna addu’ar fatan nasara, Ubangiji Allah ya taimaki mai girma Gwamna da taimakonsa, Allah ya shige masa gaba, Allah ya zama gatansa Ameen.

Amag Abdoul

Chairman Mai Palace Media Team

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment