Matasa dubu hudu (4000) za su amfana da sabon shirin Gwamnatin Jihar Zamfara (ZASIP)

Mai daraja Gwamnan Jahar Zamfara Hon (Dr) Bello Muhammad Matawalle (Maradun) zai Samawarwa Matasa 4000 ayukkanyi karkashin Sabon Shirin (ZASIP).

Mai daraja Gwamnan jihar Zamfara ya Aminta da Canzawa hukumar Matasa ta suna (YECO) zuwa (ZAMFARA SOCIAL INTERVENTION PROGRAMME) Inda za’a dauki matasa Maza da Mata guda (4000) aiki daban daban,tsarin zaiyi aiki kamar irin tsarin N-power domin rage yawan matasa da basu da aikin yi.

Kowache Mazaba zaa dauki matasa (20) da masu SSCE, DIPLOMA,NCE, DEGREE& MASTERS DEGREE.

Wadanda zasu jagoranchi wannan Sabuwar maaikata sune kamar haka;

1. Alh Usuman Dankalili Bakura- Executive Chairman
2. Hajiya Basira Musa Gusau- Director Finace and supply.
3. Alh Saidu Maishanu – PRO
4. Obama Obama – Member
5. Alh Hussaini Dan isah – Member
6. Alh. Murtala. I. Jangebe- Member
7. Alh Tukur limantawa – Member
8. Hon Kabiru Amadu Mai palace- Secretary .

Zasu fara aiki nan take domin daukar wadannan matasa aiki.

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment