Majalisar wakilai ta bukaci Buhari ya saki Sheikh Zakzaky.

Majalisar wakilan Najeriya ta yi kira ga gwamnati da ta saki jagoran kungiyar ‘Yan Uwa Musulmi ta ‘yan Shi’a kamar yadda wasu kotunan kasar suka bayar da belinsa a baya.


Majalisar ta amince da wannan kuduri ne kwana guda bayan taho-mu-gamar da aka yi tsakanin ‘yan sanda da kuma mabiya Sheikh Ibrahim Elzakazaky a harabar majalisar, lamarin da ya haifar da asarar rayuka, sannan ya kai ga dage zaman majalisar.

Honourable Abdurrazak Namdas, mai magana da yawun majalisar na riko, ya shaida wa BBC cewa a matsayinsu na wakilan jama’a suna ganin ya dace a saki jagoran na ‘yan Shi’a domin wanzar da zaman lafiya.

Tun shekarar 2015 ne ake tsare da Sheikh Zakzaky bayan wani hari da jami’an tsaro suka kai wa magoya bayansa a Zariya, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum fiye da 300.

Tun lokacin ne kuma mabiyansa ke ta zanga-zangar neman a sako shi, suna masu zargin cewa yana cikin mummunan yanayin rashin lafiya.

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment