Shawarwari 20 da Kwamitin karbar Mulki ya ba Gwamna Matawalle

Kwarya-kwaryar Shawarwar da Kwamitin Transition wato kwamitin amsar mulki yabawa Gwamnatin Matawalle domin fara gadan-gadan. Kwamitin karkashin Malam Wakkala Ibrahim

👉Shawara kan Tsaro Zamfara.

Kwamitin Transition yabada Shawara ga Gwamna Bello Matawalle, akan yacigaba da kokarin dayayekeyi akan Shawo kan matsalar tsaro babu dare babu Rana domin wannan Matsala itace babbar matsalar dake damun jahar Zamfara. Kwmaitin yace duk kalubalen da gwamna zai huskanta to ya daure dai Allah zai Shigemasa gaba. Kuma insha Allah zaiyi nasara

👉Shawara kan bin Tsarin Shariar Musulunci Zamfara.

Kwamitin Transition yabada Shawara ga Gwamna Bello Matawalle, akan yatabbatarda andawoda bin tsarin Shariar musulunci Zamfara, domin watsi da Tsarin Sharia shine ya jefa jahar cikin matsaloli dadama. Tareda tabatarda duk wanda yakamata ahukunta akan Aikin daya aikata to a hukuntashi domin hakan shine kadai zai kawo zaman lafiya zamfara.

👉Shawara Akan Albashin Maikatan Gwamnati Zamfara.

Kwamitin yabada Shawara akan Gwamnatin Matawalle, tayi duk yanda zatayi ta diba hakokan Maikatan jahar Zamfara musamman malamman makaranta da Maikatan kananan hukumomi, wanda har Yanzu akwai wadanda ake biya Albashi wanda baikai dubu 18,000 ba.

Haka aduba batun promotions, annual increments da dai sauransu domin inganta rayuwar Maikatan jahar Zamfara domin suma
Suci moriyar demoradiya.

👉Shawara akan biyan Pension da gratuities a Zamfara

Kwamitin yabada Shawara ga Gwamnatin Matawalle, akan tayiwa Allah ta duba batun biyan kudeden pension da gratuities ga tsofaffin Maikatan jahar Zamfara, da kananan hukumomin zamfara wanda sukayi raitaya, zakaga mutun yagama aiki amma har yazo ya tsufa ya mutu amma baa bashi kudinsa ba gashi talauci yayi yawa. Kuma baban abun bakinciki gwamnatin baya ta fitarda kudade da cewa wai ambiya pension Amma an chanye kudaden.

👉Shawara akan biyan Scholarship ga Yanmakaranta Zamfara.

Kwamiti yabada Shawara ga Gwamna Matawalle, akan ya fito da tsari mai kyau akan biyan kudaden Scholarship ga dalibban jahar Zamfara dake karatu manyan makarantu domin ragewa uwayensu wahalhalu wajen daukar nauyinsu.

Kwamiti yace, abinciken dayayi akwai dalibban jahar Zamfara, dadama wadanda suka kasa zuwa gaba da Sakandare saboda basuda hali uwayensu basuda halin biyamasu kudaden makaranta. Don haka suna bada shawara ga Gwamnati data rika biyan kudaden Scholarship akai akai ga Dalibban jahar Zamfara.

👉Shawara akan State University Zamfara.
Kwamitin yabada shawara ga Gwamnati akan duk dayake jahar Zamfara, nabukatar Jamia mallakar jaha domin muhimmancinta ga alummah dakuma jaha gabakidaya amma duk dahaka baikamata akaucewa tsari da dokokiba na ginin jamia da samarda jamia mai inganci da maana.

Kwamiti yace abinciken dayayi yagano cewa ita wannan University tuni har ambada admission ga dalibbai har wai dalibbai sunfara karatu amma abun mamaki wanan makaranta batada Management batada Shugabanni batada malammai kwata kwata babu wani doka ko tsari da akabi wajen fara aikin wannan makaranta. Haka abun mamaki angano cewa gwamnatin Yari tabada kwangila 100% amabiya kudi akan akawo katifu makarantar amma ko katifa ko daya baa kawoba. Don haka kwamiti yabada Shawara akan Gwamnati ta dakatarda ginin wannan University har sai anyi bincike akan yanda aka gudanarda kwangilar ginin Makarantar da samardaita. Hasalima yanzu Gwamnati na hukantar matsanacin rashin kudin da zata iya gudanarda jamiar.

👉Shawara akan Gusau Motel
Kwamiti yayi bincike akan cewa Gusau Gwamnati ta duba yadda wanan wuri yake gudana domin akwai koke akan cewa wurin ana aikata ayukkan assha marasa kyau don haka yanada kyau Gwamnati ta duba yiyuwar gyara wannan waje da chanzashe zuwa wani abu mai muhimmanci ga Alummah.

👉Shawara akan kayan Gwamnati da Bankuna ke kwacewa Zamfara. (Garnish)
Kwamiti yabada Shawara akan Gwamnati ta diba matasalar da take haddasa bankuna ke kwace dukiyar jahar zamfara take sayarwa cikin masakanar kudi.

Domin binciken da Kwamiti yayi ya gano cewa yanzu haka akwai cases 24 dake gaban kotuna tsakanin gwamnatin jahar Zamfara da bakuna da wasu kampanoni saboda taurin bashi. Don haka kwamiti yabada Shawara da Gwamnati ta zauna da wadannan bankuna da kampanoni su fahimci juna domin sasantawa domin kada kotu tasake basu dukiyar jahar Zamfara suna sayarwa walakance.

👉Shawara akan Maaikatar Ruwa zamfara

Kwamiti yabada Shawara akan Gwamnati tayi binceke sosai akan maikatar ruwa ta jahar Zamfara, domin akwai badakaloli da cuwa cuwa sosai wajen sayen Alam da chemicals da sauransu wanda hakan ya jawo dukda kudaden da ake kashewa maikatar amma baa samun ruwansha wadatattu ajahar.

👉Shawara Kan Iimi zamfara
Kwamiti yabada Shawara akan Gwamnati tayi kokari ta gyara matsalolin ilimi dake addabar jahar Zamfara wajen cigaba da gyara makarantu tabbatarda yaran jahar Zamfara kowa yaje makaranta kuma yasamu ingattacen, kula da malammai da albashinsu bada tallafin karatu da matasllafan ilimi ga makarantu da dalibban jahar Zamfara.

👉Shawara akan Halal Hotel dake Abuja Mallakar jahar zamfara.

Kwamiti yabada shawara akan gwamnati data qdtbincika akan ayukkan wannan Hotel domin hotel din yanzu haka yana karakashin wani kampani wanda idan Gwamnati bata dauki matakiba to wannan hotel zai kubucewa jahar Zamfara, kuma wannan hotel yanada muhimmanci ga tattalin arzikin jahar zamfara musamman a inda yake da location nashi.

👉Shawara kan bada Kwagiloli zamfara

Kwamiti yabada Shawara akan gwamna yadiba yadda aka bada kwangiloli zamfara domin mafiyawa baabin dokoki kuma ba abin tsari wanda hakan Kesa ana bada kwangiloli yan kwangiloli na aiki babu inganci cikin kankanin lokaci yalalace. Don haka Gwamna yayi iyakacin is kokarinsa domin inganta wajen.

👉Shawara akan Kaddarorin Gwamnati Zamfara

Kwamiti yabada Shawara akan Gwamnati data saka ido sosai akan kadarorin Gwamnati domin wasu na kokari mallakawa kawunansu dokiyoyin Gwamnati don haka Gwamnati ta dauki matakin kare kadarori da dukiyar Gwamnati.

👉Shawara akan 1400 workers da aka dauka aiki

Kwamiti ya yabawa Gwamnati akan kokarin datayi na dawo da maikata 1400 aiki wanda hakan ya nuna yanda gwamnatin Matawalle keson yaki da zaman banza jahar zamfara.

Kwamiti yabada Shawara akan binciken da sukayi sungano cewa acikin wadannan maitaka wasunsu sun samu aikinyi yakamata abincika da kyau domin tantance wadanda ke wani aiki domin cire sunanayensu sukuma wadanda basu wani aiki abasu posting suje sucigaba da aiki afara biyansu cikin lokaci.

👉Shawara akan Aikin Gwamnati da Maaikatun Gwamnati
Kwamiti yabada Shawara akan Gwamnati ta diba dokokin da suka kafa wasu maikatun Zamfara cikin maaikatun jahar Zamfara wadanda suka hada Agencies, parastatals da sauransu akwai wadanda ko dokoki basuda, akwai wadanda babu maikata wajen amma anabiyan albashinsu, akawai wadanda akwai maikata amma basu zuwa aiki wuri, akwai wadanda ga maikatan amma babu aiki. Akwai maikatunda yakamata suyi aiki tare basai an rabasuba.

👉Shawara akan Hukumar Alhazzai
Kwamiti yabada Shawara akan Gwamnati tayi bincike akan badakaloli da cuwa-cuwa da rashin bin dokoki a hukumar.

Binciken da Kwamitin yayi yagano cewa yanzu haka akwai alhazzan da suka kwashe shekara 7 dabiyan Hajji amma anchanye kudadensu kuma har yanzu basuje hajjinba kuma baa biyasuba.
Donhaka kwamiti nabada shawara akan gwamna ya mayarda hankali sosai akan hukumar domin kare martaba da mutuncin alhazzan jahar Zamfara.

👉Shawara akan diba yanda akayi nade naden mukaman Permanent Sakatarosa da sauransu

Kwamiti bada shawara akan Gwamnati ta binciki nade naden mukamai da tsohuwar Gwamnati tayi gab da cikas waadinta domin duba ko andaukesu kan kaida kokuwa dai baadaukesu kan kaidaba.

👉Shawara akan Cigaba da aikin tsohuwar Gwamnati tabari.

Kwamiti yabada shawara akan Gwamnatin matawalle ta duba ayukkan da tsohuwar Gwamnati datayi masu muhimmanci domin cigaba dasu.

Kwamitin ya yabawa tsohuwar Gwamnati akan yadda tagina Tituna, Makarantu, asibitoci dasauransu don haka sun shawarci gwamnatin Matawalle itama tayi koyi da gwamnatin Baya wajen cigaba da wadannan ayukkan bunkasa jaha.

👉Shawara akan bunkasa rayuwar Matasa
Kwamitin yabada shawara akan Gwamnati data bullo da hanyoyin samarda ayukka ga matasan dasuka kammala karatu domin suma su samu harkaryi su zama masu dogaro dakansu wanda hakan zai rage radadin rashin ayukkan yi da zaman banza tsakanin matasan jahar zamfara.

👉Acikin Rahoto kwamitin ya bayyanawa Gwamnati cewa gwamnatin data gabata tabar liabilities, ta handame kudade da aikata badaidaba da dukiyar jahar dayawanta yakai Biliyan 300bn.

Wadannan kadan daga cikin Shawarwarin gaggawa da Kwamitin amsar Gwamnati ya bayar ga gwamnati domin Gwamnati tafara aiwatarda aiki kafin cikakken Rahoto da bayanai.

Rahoton Ubaidullah Yahaya Kaura
Blogger

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment