Za mu tabbatar mun mika duk wanda muka samu da hannu wajen badakalar albashin jihar Kano

Za mu tabbatar mun mika duk wanda muka samu da hannu wajen badakalar albashin jihar Kano gaban shari’a/Muhuyi.

Hukumar yaki da almundahana ta jihar Kano ta bayyana cewa za ta binciki yadda ake biyan ma’aikatan jihar albashi.

Shugaban Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado ya ce binciken ya zama dole saboda yadda wasu ma’aikata ke ganin ana tura masu kudade masu yawa akan albashin su.

Magaji Rimin Gado, ya ce suna zargin akwai wata makarkashiya dake gudana a wajen biyan ma’aikatan jihar, saboda haka akwai bukatar a binciki lamarin.

Ya ce hukumar ta gano akwai ma’aikatan jihar da ake biya kudade fiye da albashinsu, kuma hukumar ta sami labarin cewa wasu manyan ma’aikata da ma’aikatu da hukumomin gwamnati na ansar karin kudi fiye da albashin su.

Daga karshe ya yi kira ga ‘yan Najeriya su ba hukumomin yaki da hana cin hanci da rashawa goyan baya domin magance annobar cin hanci da rashawa.

DAGA: Mu’azzam Yakubu Sanka.

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment