Wani jami’in Custom na Najeriya mai suna Nura Dalhatu wanda yake da mukamin ASC1 dan asalin jihar Katsina ya kara ma kansa girma zuwa mukamin CGC.
Kai tsaye ya nufi hedikwatan Custom da ke Abuja ya kuma ziyarci shugaban hukumar, Com Hameed Ali a ofishinsa don ya amshi mukamin daga hannunsa a matsayin sabon shugaban hukumar bisa umurnin Shugaban kasa Muhammadu Buhari kamar yadda ya fada.
Tuni dai aka kama shi.