Gwamnatin Jahar Zamfara Zata Dauki nauyin Dalibai su yi karatun likitanci a Jami’o’in Najeriya da kashen waje.

Mai Daraja gwamnan jahar Zamfara, Hon. Dr. Bello Mohammed, Matawallen-Maradun ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta dauki ‘yan assalin jahar Domin su yi karatun likitanci da sauran kwasa-kwassan kiyon lafiya a jami’o’in kasarmu Najeriya da na kasashen waje.


Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin ‘ya’yan kungiyar likitoci Reshen jahar Zamfara wato Nigeria Medical Association (NMA) a turance, da su ka kawo masa ziyarar taya murna a fadar Gwamnatin jahar Zamfara da ke Gusau.

Gwamnan ya bayyana cewa yana daga cikin gudurinsa, na farfado da sha’anin kiyon lafiya da ya yi matukar gurgurcewa, Dan haka gwamnatinsa take zimmar daukar nauyin karatun ‘yan assalin jahar Zamfara Domin karatun bangaren likitanci da sauran kwasa-kwassan kiyon lafiya .

In dai ba a manta ba Tun a ranar karbar ranstuwar gwamnan ya yi alkawarin cewa Mata Da kananan yara za su mori kula da lafiyarsu kyauta. Sai dai haka ba zai samu ba sai an samu wadatattu jami’an kiyon lafiya da kayan aiki isassu.

Dan gane da neman da ‘ya’yan kungiyar su ka yi na Gwamnatin jahar Zamfara ta aiwatar da shirin nan na CONMESS Da zai gyara albashin likitocin Da ke aiki jahar Zamfara. Gwamnan ya yi alkawarin zai dubi llamarin.

Ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa za ta yi aiki kafada-da-kafada da ‘yan kungiyar. Domin habbaka sha’anin kiyon lafiya na jahar Zamfara, zuwa matakin kasa-da-kasa ta yadda al”ummar Zamfara za su amfana.

Haka zalika gwamnan ya bayyana cewa tuni dai ya umurci ma’aikatar kiyon lafiya, da ta turo masa Da bayanan assibitocin jahar Zamfara da abunda assibitocin su ke bukata Domin dacewa da Zamani. Da kuma kayan da ke kasa a cikin assibitocin.

Tun da farko shugaban kungiyar na jahar Zamfara, Dr. Kabiru Musa ya bayyana cewa sun zo a fadar Gwamnatin ne, Domin domin taya gwamnan murna akan nasarar da ya samu na zama gwamnan jahar Zamfara, Dan haka ya roki Allah ya rikawa gwamnan ya Sanya albarka a jagorancinsa.

Shugaban kungiyar, ya yi amfani da wannan damar inda ya jawo hankalin gwamnan jahar Zamfara. Akan mawuyacin halin da membobinsa ma’aikatan kiyon lafiya su ke ciki, idan aka daidaita su da takwarorinsu da ke a makwabtan jahohi, ta fuskar albashi, da rashin kayan aiki a dukannin Manyan assibitocin jahar dama kananan assibitocin, Wanda haka ya taimaka matuka gaya ga rashe-rashen da ake samu na musamman ga Mata masu haihuwa. Wanda ya baiwa gwamnan bayanan wadannan matsalolin a rrubue.

Yusuf Idris GUSAU

Babban Daraktan Watsa Labarai Labarai A Fadar Gwamnatin Jahar Zamfara

Fassara: Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau.

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment