Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya ziyarci takwaranshi gwamnan Zamfara.

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal yayi Kira ga alummar jahar Zamfara da su kawar da banbanci siyasa su hada kai su ba gwamnatin Mutawallen Maradun goyon baya domin ciyar da jahar gaba.


Tambuwal yayi wannan kiran ne lokacin da ya kai ziyarar sada zumunci da nuna goyon baya ga takwaranshi na jahar Zamfara a fadar gwamnatin jahar da ke garin Gusau a jiya laraba.

Ya jaddada bukatar da ke akwai na alummar jahar su hada kai ayi aiki tare batare da nuna banbancin jamiyya ba,domin samun mafita kan matsalar tsaro da ake fama da ita a jahar.


Gwamnan haka ma yayi Kira ga alummar jahohin Sokoto da Zamfara da su rika ba jamian tsaro hadin kai ,a kokarin da suke na magance matsalar tsaro a wannan yankin.

Ya taya murna ga sabon Gwamnan tare da rokon Allah ya ci gaba da yi mishi jagora wurin gudanar da shugabancin jahar Zamfara.


Da yake jawabi Gwamnan jahar Zamfara Dr Bello Mohammed Mutawalle ya godewa Gwamnan jahr Sokoto kan wannan ziyarar,tare da bada tabbacin cewa zasuyi aiki tare ba kama hannun yaro domin samun mafita kan kalubalen da ake fuskanta fannin tsaro a jahohin Sokoto da Zamfara.

Governor Bello ya ce gwamnatinsa na iya kokarinta don ganin ta dakile abubuwan da yan taadda ke aikatawa a jahar , ya kara da cewa bada dadewa ba,zaa ji sakamakon tattaunawar da sukayi da fulani makiyaya.

Tun da farko tsohon gwamnan jahar Sokoto Alh Attahiru Dalhatu Bafarawa Kira yayi ga alummar jahohin biyu da su ci gaba da yiwa shugabannin su addua domin samun nasara,ya kuma taya su murnar samun Mutawallen Sokoto da Mutawallen Maradun a matsayin shugabannin su.

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment