Gwamnatin Jahar Zamfara za ta samar da rugagen fulani.

GWAMNATIN JAHAR ZAMFARA, ZA TA SAMAR DA RUGGAR FULANI UKU, DOMIN TALLAFAWA YUNKURIN GWAMNATIN TARAYYA NA SAMAR DA TSARO.


Gwamnatin jahar Zamfara, ta yi shirin Samar da ruggagen Fulani guda uku, Domin marawa shirin gwamnatin Tarayya na Samar da tsaro a lungu da sako na kasar nan.

Gwamna Hon Dr Bello Mohammed Matawalle ya bayyana haka ne a wurin taron shuwagabannin hukumomin tsaro da shuwagabannin Miyyeti Allah Cattle breeders Association of Nigeria, tare da shugaban ‘Yan sa-kai da ‘yan banga. Wanda ya gudana a Sakateriyar Jibril Bala Yakubu da ke Gusau.

Gwamna Matawalle ya bayyana cewa gwamnatinsa ta samar da dukkanin kudaden da shirin zai bukata. Tare da zana yadda shirin zai kasance domin tuntubar Fulani da hada kawunansu, Domin samar da ruggar Fulani daya a dukkanin yankuna uku na jahar Zamfara.

Ya Kara Da cewa filin hekta 100 ne za a yi amfani Da shi a Kowane yanki na jahar Zamfara, tare da samar da kayayyakin more rayuwa wadanda suka da korammu, makarantannin firamare da sikandire, makarantannin islamiya Da kuma Assibitoci biyu-biyu na mutane da dabbobi.

Makasudin yin wannan shirin na rugga shi ne, Domin marawa shirin Gwamnatin Tarayya. Karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari na kawo karshen matsalar tsaron da ke addabar jahar Zamfara da Najeriya baki daya.

Matawallen ya Kara Da cewa, domin samar zaman lafiya Mai dorewa Gwamnatinsa za ta kafa kwamiti Wanda zai kunshi jami’an Gwamnati, wakilai daga hukumomin tsaro na jahar Zamfara, shuwagabannin Fulani, ‘Yan sa-kai Da sauran masu ruwa-da-tsaki akan sha’anin tsaro. Domin Tattaunawa akan yadda za a kawo karshen matsalar tsaron jahar Zamfara.

Gwamna Matawalle ya bayyana muddun aka yi haka to matsalar tsaron jahar Zamfara za ta zama tarihi.

Ya Kara Da cewa, matsalar tsaron jahar Zamfara, da ta ki ci ta ki cinyewa, ta taka rawa matuka gaya wajen hada cigaba jahar ta fuskar tattalin arziki da kuma walwalar Al’umma. Dama duk wani Abu na cigaban jahar .

Gwamna Bello Mohammed ya bayyana cewa wannan shirin zai taimaka matuka gaya, ga al’ummar da ayukkan ‘yan ta’adda, ya jefa su cikin halin ni-‘yasu. Wanda nan ba da dadewa ba matsin Da su ke ciki zai sama tarihi. ya Kara Da cewa gwamnatinsa za ta Samar da gandun daji da makiyaya za su samu damar kiyon dabbobinsu a tsanake.

Dangane da Mika makaman ‘yan ta’addan, gwamnan ya yi Kira ga duk Dan ta’addan da ke da sauran makami a tare da shi, to ya yi gaugawar mika shi ga hukuma, Domin baiwa baiwa gwamnati damar tattaunawar zaman lafiya. “Domin Gwamnatina a shirye take Domin hada Kai da ‘yan bindigar da suka tuba, Domin Samar da zaman lafiya. Wadanda kuma su ka ki to gwamnati shirye take ta yake su da karfi”.


Daga karshe gwamnan ya yi Kira ga al’ummar da su ka bar matsugunnansu, zuwa wasu jahohin da su dawo gida, domin gwamnati za ta iya iya yinta wajen kariyar rayukka da dukiyoyin al’ummar jahar Zamfara.

YUSUF IDRIS G

Babban Daraktan Watsa Labarai A Fadar Gwamnatin Jahar Zamfara .
Fassara: Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment