Dalibab makarantar Al-qalam da ke katsina sun kunyata Shehin malami Mufti Menk.

Daliban makarantar Al-Qalam Katsina sun kunyata ni – Mufti Menk.


Fitaccen Malamin Addinin Musuluncin kuma shugaban masu fada fatawa na kasar Zimbabwe, Mufti Isma’il Menk wanda yayi suna a kowanne lungu da sako na duniyar, ya bayyana rashin jin dadin shi akan irin yadda daliban makarantar Al-Qalam Katsina suka nuna rashin da’a a gareshi.

Ga kalaman da Jaridar Dabo FM ta binciko wanda Mufti Isma’il Menk yayi.Wallahi baku yiwa kanku adalci ba, ni a matsayin uba nake a gareku, kuma dole na fada muku gaskiya. Gaskiyar magana ita ce kunyi surutu wanda ya wuce tunani, kuma hakan yasa kun bani kunya matuka.

Saboda haka zan tafi, sai Allah ya kara hadamu watarana idan da rai da lafiya, Allah yayi muku albarka baki dayanku.

Bayan hira da wani dalibin makarantar da yayi da manema labarai, ya bayyana cewa, Malamin ya fara gabatar da fatawa ne sai surutun dalibai yayi yawa, hakan yasa dole ya katse fatawar tasa ya kuma fice.

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment