‘YAN BINDIGA SUN MIKA WUYA TARE DA TATTARO MAKAMAN SU A JAHAR ZAMFARA.

‘Yan bindigar Zamfara da yawa sun tuba, sun mika bindigu 216 – Gwamna Matawalle

A ranar lahadi ne gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya bayyana cewa da dama daga cikin ‘yan bindigar da suka hana jihar zama lafiya sun tuba, tare da mika wa gwamnati bindigu 216, yawancinsu samfurin AK47.

Hakan na kunshe ne a cikin wani jawabi da Yusuf Idris, babban darektan yada labaran gwamna, ya fitar ranar Lahadi, a Gusau, babban birnin jihar Zamfara.

Sanarwar ta bayyana cewa gwaman ya fadi hakan ne ranar Asabar yayin da ya karbi bakuncin tsohon shugaban kasa, Janar Yakubu Gowon, a gidan gwamnatin jihar da ke Gusau.

A cewar sanarwar, ‘yan bindigar sun mayar wa gwamnati bindigunsu da sauran makamai ta hannun wasu tubabbun ‘yan bindigar da suka lashi takobin taimaka wa gwamnatin a kokarinta na dawo da zaman lafiya bayan sun tuba daga aikata miyagun laifuka.

Gwamnan ya bayyana ziyarar Gowon a matsayin karrama wa gare shi tare da neman shawara daga gare shi a kan yadda zai kawo karshen ‘yan bindiga a jihar.

A bangaren kokarin da gwamnatinsa ke yi wajen kawo karshen aiyukan ‘yan ta’adda, Matawalle ya ce gwamnatinsa ta dauki matakai da yawa da suka hada da yin sulhu, wanda ya ce sakamakon hakan, yanzu wasu ‘yan bindigar da yawa sun tuba tare da mika bindigunsu samfurin AK47 guda 216 ga hukuma.

A nasa bangaren, Gowon ya ce ya ziyarci jihar ne domin gudanar da addu’o’in neman zaman lafiya a yankin arewa maso yamma da Najeriya ‘baki daya’.

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment