NASARA DAGA ALLAH, SOJOJI SUN CIKA ALWASHIN DA SUKA SHA. CIKAR WA’ADIN DA JIMI’AN SOJI SUKA BA ‘YAN BINDIGA A JIHAR ZAMFARA NA SA’O’I 24 YA CIKA, SOJOJI SUN FARMA ‘YAN BINDIGA 29 SUKA CIKA.

A kalla ‘yan bindiga 29 ne dakarun sojojin atisayen Operation Hadarin Daji suka kashe yayin harin da suka kai a dajin Moriki na Jihar Zamfara. Mai magana da yawun Rundunar Sojojin, Laftanat Oni Orisun ne ya tabbatar da hakan yayin zantawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa a ranar Alhamis a garin Gusau.


Ya ce “dakarun sojojin sun farwa ‘yan bindigan ne bayan cikar wa’addin sa’o’i 24 da kwamandan sojojin, Manjo Janar Jide Ogunlade ya bawa ‘yan bindigan su ajiye makamansu su rungumi zaman lafiya. “Kwamandan sojojin ba wasa ya ke yi ba yayin da ya ce sojojinsa za su far wa ‘yan bindigan idan wa’adin da aka basu ta cika. “An rufe dukkan hanyoyin da za su bi su tsere wadda hakan yasa ‘yan bindigan yin musayar wuta da sojojin.

“Dakarun sojoji biyu da dan sanda guda daya sun rasu yayin artabun. “Rasuwar jami’an tsaron uku abin bakin ciki ne musamman ga kwamandan sojojin, Manjo Janar Jide Ogunlade sai dai ya yi imanin atisayen da suke gudanarwa za ta kawo karshen ‘yan bindigan da ke jihar,” inji Orisun.

Wanni shaidan ganin ido, Mallam Lawali Moriki ya shaidawa NAN cewa “muna ganin jami’an tsaro da yawa suna kai da komowa a cikin kwanakin nan.

“Bayan hakan mun ji karar bindigu daga cikin dajin da ke garin mu kuma mun ga gawarwakin ‘yan bindiga da dama ana wucewa da su cikin motoccin jami’an tsaro.”

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment