SAURA TAKWAS YA CIKA TAKWAS FAIL ZA MU BASHI KO PASS

Saura kwana takwas kacal Gwamna AA yari ya cika shekara takwas cif yana mulkin Jihar Zamfara, a ranar 29/05/2019 mai zuwa itace ranar da wa’adin mulkinsa zai kare wanda zai mika mulkin ga wanda zai gajesa na hannun damarsa ko kuma waninsa babu dai makawa a wannan ranar mulkin zai fita da ga hannunsa.

Yawanci idan shugaba zai sauka da ga mulki zaka samu al’ummar da yake mulka suna cikin alhini wasu harda kuka saboda tsanin so da shakuwa da jindadin mulkinsa, amma sai dai kash! Banda jihar Zamfara, tun tsawon watannin da suka wuce mafi yawancin al’ummar Jihar Zamfara suka dukufa wajen lissafin adadin kwanaki da awanni da mintunan da suka ragema AA yari.

A halin yanzu saura takwas ya cika takwas:- Wasu kadan da ga cikin abubuwan da baza’a mantaba a mulkin AA Yari↓

◈ A cikin mulkinsa ne dubban dubatar mutane suka rasa rayukansu ta sanadiyar tabarbarewar tsaro wanda tun wa’adinsa na farko aka fara yima al’ummar jihar Zamfara kisan kiyashi

◈ Mata sun rasa mazajensu an samu yawaitar marayu ga ‘Yan gudun hijira ba’a kyautata rayuwar su yau babu sansanin ‘Yan na ‘Yan gudun hijira, suna nan sun shiga cikin garuruwa.

◈ A cikin mulkinsa dubban al’umma sun rasa muhalansu, dukiyarsu an talautasu.

◈ A cikin mulkinsa matasa sun rasa kyakkyawar makoma rashin aikin yi ba’a kula da muradunsu.

◈ A cikin mulkinsa ma’aikata an maida Su ba
kowaba ya karyasu ya hana masu hakkoansu.

◈ A cikin mulkinsa Jihar Zamfara ta kasance jiha ta daya da tafi kowace jiha talauci a fadin Nigeria ta kasance ta baya a wajen neman ilimi

◈ A cikin mulkinsa kasuwanci ya mutu mutus yau babu wata kasu da ake bugun gaba da ita a jihar Zamfara

◈ A cikin mulkinsa ‘yan majalisar dokoki suka zama kaskantattu wanda har jigogin majalisar sukayi yunkurin tsigeshi ya sa aka kamasu.

◈ AA yari ya karya kowa an kakabawa al’ummar jihar Zamfara mummunan talauci wanda yasa suka manta da me ake cema ‘yanci.

◈ AA yari ya karya manoma babu wani tallafi da manoman jihar Zamfara suke samu a cikin mulkinsa

◈ A cikin mulkinsa ya yima duk wata doka karan tsaye babu wani abu da ake shimfidawa jihar Zamfara a bisa doka domin ko ‘Yan majalisa masu doka sun sha duka wanda karshe suka zama karnuka.

Abubuwan suna da yawa tabbas ba za’a manta da ukuba da tashin hankali da halin rashin tabbas da aka shigaba a mulkin Gwamna Abdulaziz Abubakar Yari inkiya Shehi.

Me za mu bashi

❌FAIL KO PASS ✅

DAGA: Abdulsamad Kabiru Musa

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment