Zunuban boye su ne manyan hatsari a rayuwar musulmai

Godiya ta tabbata ga Allah, majibincin dukan al’amurra.

Tsira da aminci su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammadu, da alayenSa da sahabbanSa baki daya.

Bayan haka, lallai gaskiya –kamar yadda ake fadi- daci ne da ita!.


Mai yiwuwa babban dalilin dacinta shi ne, abin da mai bincikenta yake gamuwa da shi akan hanyarsa ta bincike, na fuskantar soke-soke, da karyata abin da yake faruwa a rayuwar yau da kullum na mutane.

Kuma babu abin da zai rage wannan dacin –ba zan ce ya ga bayansa ko ya kawo karshensa baki daya ba- sai an shimfida cikakken “ikhlasi” da yin abu saboda Allah, akan hanyar biciken wannan gaskiyar, ta yadda wannan binciken zai zamanto bincike ne da ya kubuta daga dukan wasu manufofi –wadanda ba su da wata dangantaka da wannan binciken- na nesa da na kusa.

Lallai idan mai binciken gaskiya ya yi riko da wannan hanyar, tabbas ya yanki hanzari a gaban Allah (Subhanahu wa Ta’ala) da gaban bayinSa. Babu komai a gare shi, idan ya gaza wajen juya dabi’un abubuwa, misali, a ce ya gaza wajen juya dacin magani ya komar da shi zuwa zakin suga.

Lallai komai nauyi da dacin da ke tattare da gaskiya, riko da ita ya fi yi wa mutum da al’umma amfani akan a guje mata, balle a ce su kama husuma da fada da ita.

Ya isa mai bincike yin uzuri -idan ya yi riko da wannan hanya- cewa shi ba ya tilasta wa mutane wahalar riko da gaskiya, sai abin da shi ma ya tilasta wa kansa, kuma ba ya dandana masu dacinta, face abin da shi ma tuni ya riga ya dandana kafin su dandana. Kuma shi bai mayar da kansa kaman Annabin da ba ya laifi ba, wanda zai rinka saukar masu da shiryatarwarsa daga kan minbarin “Isma(*)”, sannan zatinsa ya cigaba da zama tsarkakakke daga laifi ba, a’a, shi ya sanya wa kansa ido ne, domin neman yanda zai gyara kura-kurensa, sannan kuma ya fadakar da sauran jama’a, akan kada su bace irin bacewar da ya yi, kar su yarda su yi kuskure irin kuskuren da ya yi.

Kuma wannan wani kokari ne daga gare shi, domin ya jiyar da abokansa da ‘yan-uwansa dadin nasiha da shiriya, kamar yadda Allah Madaukakin Sarki Ya karrama shi da jin dadin haka.

Shin a cikin wannan maganar akwai wata alamar bata ko rudani?!..

====

* Abin da ake nufi da “Isma” ko kuma idan an ce: “wane ma’asumi ne” shi ne: Allah Ya bai wa wane kariya ta musamman wadda za ta katange shi ga barin aikata abin da Allah Ya hana aikatawa na zunubai, babu wanda yake samun wannan matsayi daga cikin bil-adama sai Annabawa da Manzanni (A.S) don haka “Isma” ita ce kariyar da Allah (Subhanahu wa Ta’ala) Yake bai wa Zababbu daga cikin bayinSa. (Kaura)..

******

Sheikh Muhammad Sa’id Ramadhan Al- Bouti (RahimahulLah)..

Tarjama: Saleh Kaura

© TASKAR SUNNA

ZUNUBAN BOYE SU NE:
Manyan Hatsari A Rayuwar Musulmai

-02-

Lallai akan wannan turbar ce na gina binciken da na yi a wannan littafin, hakika- Allah Ya sani- na yi nufin yi wa kai na nasiha ne, kafin in nufi kowa da ita.

Amma duk da haka wasu sun kuntata da wannan binciken, domin ya yi suka akan salon yadda suke gudanar da rayuwarsu, sannan kuma ya yi kokarin gyara halin da suke rayuwarsu ta yau da kullum akai. Sakamakon wannan kuntata tasu ne, abubuwan ban mamaki suka faru, wadanda nan ba wurin maganarsu ne, ba kuma wata fa’ida ko amfani idan an yi magana akansu.


An yi mini magana kan matsayin wadannan mutane. Sai na ce –kuma abin da ne fadi shi ne gaskiyar da ban san waninsa ba-:

In dai “Isma” ce, wato kubuta daga aikata kuskure, to ni ban san wani mutum da ya sifantu da ita ba, bayan Manzanni da Annabawa (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare Su)!!..

Amma kin nasiha, da yin girman kai wajen karbarta, ban san wani Musulmi, mai gaskiya a Musuluncinsa da zai amince wa ransa, kan ya dare kan kujerar yi mata girman kai ba!!.

Amma salo, ko hanya mafi kyau wajen tseratar da nasihar gaskiya, lallai ba mu da wata hanya ko salo, sai salon fiyyayen talikai, Muhammadu Mai tsira da aminci.

Lallai Ya kasance mai nasiha ne, yana mai karantar da sahabbanSa kan cewa: Addini nasiha ne.

Yana warware ayyukan mutane ta hanyar fitar da masu kyau da marasa kyau, ba tare da Ya ambaci sunaye, ko Ya tozarta wasu ba, cewa Yake yi: ((Mene ne ya sanya wasu mutane….)) Sannan bai damu da matsayin wannan suka tasa, kan ta yaya za ta fada cikin zukatan mutane gaba dayansu ba.

Amma yiwuwar a sami kuskure a cikin abin da na rubuta kuwa, wannan abu ne wanda na cika kunnuwan al’umma da shi, kan ko na sami gyarar kuskuren da na yi daga makaranta, ko su tuna mini abin da na manta ban fada ba, ko su fadakar da ni kan wata gaskiya ta ilimi, wadda iliminta ya kubuce mini. Sai dai ni har yanzu ban sami hakan ba, sai ta bangaren binciken da na yi masa suna (Matsalarmu ta dabi’u ce, ba ta tunani ba.) lallai na sami wanda yake cewa: “a’a Matsalarmu ta tunani ce, ba ta dabi’u ba!..). na sami abin da suka rude akansa, suka kuma kasa fahimtar abin da nake nufi.

Cewa suke yi, wai ni ina kira ne zuwa ga tsantsar dabi’un da ba ruwansu da tunani ko ilimi, wai shela da yekuwa nake yi, kan cewa: wai su ba sa bukatar wani tunani, ko ilimi!.

Hakika ni ban rubuta wata magana mai nuni zuwa ga haka ba har abada. Duk mai gano ma’anoni daga cikin lafuzza ta hanyar bin ka’idojin harshe, ba zai fitar da irin wannan batacciyar magana –da ba zai taba yiwuwa na fadeta ba– daga cikin maganar da na rubuta a wannan babin ba.

Duk da haka, zan yi karin bayani a wannan bugun -in Allah Ya yarda- zan kuma yi karin haske akan duk wani abin da ba a gane ba a sakamakon rashin fitowarsa fili, ko sakamakon rudewar makaranta.

Sheikh Muhammad Sa’id Ramadhan Al- Bouti (RahimahulLah)..

Tarjama: Saleh Kaura

© TASKAR SUNNA

ZUNUBAN BOYE SU NE:
Manyan Hatsari A Rayuwar Musulmai

-03-

Idan haka ne, to gani zan sake buga wannan littafin, a lokacin da nake cikin tsananin yarda da farin-ciki, da dacewar da Allah Ya ba ni a cikin wannan littafin.. kai, zan sake buga wannan littafin, ina mai yawaita godiya ga Allah (Subhanahu wa Ta’ala) da Ya sanya shi ya zama tsanin amfani da gyara ga jama’ar Musulmai masu dimbin yawa, mai yiwuwa ma ni na fi su bukatuwa zuwa ga wannan amfanin da gyarar.

Zan sake buga shi a lokacin da abubuwan da suke faruwa da Musulmai na munanan masifu a kullum suna kara mini tabbacin cewa, lallai Musulmai a yanzu jan su ake yi -a rarrabe cikin kaskanci da wulakanci- zuwa baya, ba domin komai ba, sai don abin da suka boye na zunubai, wanda hatsurransu sun fi na zahirin abin da suke aikatawa na zunubai..


Zan sake bugawa, a lokacin da rashin dadin halin da Musulunci ya kasance a ciki yake kara mini tabbacin -a kullum- kan cewa: lallai matsalar Musulmai na faruwa ne saboda bala’in da ya same su a dabi’un su, ba wai wata matsala ko rudewa a cikin wayewarsu ba.

Wannan kenan, duk da ina da tabbacin cewa lallai babu yadda za a iya a ce Musulmai sun rayu ba tare da ilimi da wayewa ba, kamar dai yadda mara lafiya ba zai rayu ba idan babu rana, babu iska; sai dai fa rana da iska wani abu ne daban, shi kuma maganin da zai gyara halin mara lafiya wani abu ne daban.

Zan sake buga wannan littafin -Allah Yana shaida- kan cewa: ban rubuta wannan littafi domin yada kiyayya, ko kuma saboda keta, ko aibata wasu jama’a ba, ta yaya ma za a ce na yi haka, bayan yin hakan mummunar abu ne, wanda ban rubuta wannan littafin ba sai domin tsoratar da jama’a hatsarin dake tattare da shi, da kuma tsarkake zukata daga sharrinsa.

Amma duk da haka, ganin cewa akwai wannan annoba mai hatsari a gaban al’umma, da ganin yadda take barna a cikinsu (ba wani abu ne al’umma ba, sai ni da kai da shi); don haka ne, nake son na fadakar game da wannan annobar, ta hanyar bayanin da ba shi da wata fassara –in Allah Ya yarda- ban da cewa: Nasiha ne saboda Allah da ManzonSa da Muminai baki daya.

Zan sake bugawa, a lokacin da nake shimfida hannaye na zuwa ga Masanin abin da yake boye, cikin tsananin kaskantar da kai, ina mai rokonSa Ya tabbatar wa da Musulmai abin da Ya riga Ya sanya shi ne sifofinsu da suka bambanta da kowa da su: ((Ya Ubangijinmu Ka gafarta mana, mu da ‘yan-uwanmu da suka rigaye mu yin imani, kada Ka sanya kin wadanda suka yi imani a cikin zukatanmu, lallai kai mai yawan tausayi da rahama ne.)

Sheikh Muhammad Sa’id Ramadhan Al- Bouti (RahimahulLah)..

Tarjama: Saleh Kaura

© TASKAR SUNNA

ZUNUBAN BOYE SU NE:
Manyan Hatsari A Rayuwar Musulmai

-04-

SHIMFIDA:

Ya Ubangiji, godiya ta tabbata a gareKa daidai da yadda ta dace da girman zatinKa, da kuma girman mulkinKa, mun ambaci tsarkinKa ya Ubangiji, ba zan iya iyakace yabo a gareKa kamar yadda Ka yabi kanKa ba.

Ya Ubangiji, Ka yi fiyayyen salatinKa ga BawanKa kuma AnnabinKa Muhammadu, da AlayensSa da MatanSa da Sahabbai, kamar dai yadda Ka yi salati ga Ibrahim da AlayenSa a cikin talikai, lallai Kai abin a yi maSa godiya ne, Mai kuma kyautatawa.

Ya dan-uwana Musulmi, hakika ka tambaye ni a halin kana mai jin kuna da damuwa, kana mai cewa:

Lallai yawan Musulmai -a yau- ya fi na dukan zamunnan da suka wuce, na kusa da na nesa, kuma kokarinsu wajen yin aikin Musulunci a zahiri ya fi na kowane zamani da ya gabata. Dakunan karatu cike suke da littafan Musulunci mabambanta kuma na zamani, ta inda za ka iya cewa: ba a taba samun dakunan karatu a cike kamar yadda aka samu a wannan zamanin ba, sannan ba yawan ne kawai ba, mutane ma sun dukufa ka’in da na’in wajen karanta su, abin gwanin ban sha’awa!!.

Amma duk da haka, kokarinsu na samar da al’umma Musulma, mai aiki da hukunce-hukuncen Musulunci sai cibaya yake yi, yana kuma komawa, abin kamar da wuya gurguwa da auren nesa!.

Wannan sabanin mai matukar ban mamaki, wai mene ne sirrinsa ne…. ta yaya ne aka yi wannan bishiyar ta kasa bayar da ‘ya’yanta kamar yadda aka saba..?!

Hakika a cikin amsar da na ba ka, na ce maka: Lallai su ba wani abu ba ne face abu ne da yake a rarrabe, kana kuma ga shi duk sun juya wa junansu baya, kuma ita rarrabuwa ai bala’i ce mai bata dukan ayyuka na gari, ta kuma yanke mafi yawan ‘ya’yan da ake tsumaya tun kafin su nuna, to ina kuma a ce wannan rarrabuwar ta hadu da juya wa juna baya?!.

Sheikh Muhammad Sa’id Ramadhan Al- Bouti (RahimahulLah)..

Tarjama: Saleh Kaura

© TASKAR SUNNA

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment