Yadda zata kaya gobe zaman shari’ar APC Zamfara kotun ALLAH ya isa

Gobe ne in ALLAH ya Kai mu, kotun kolin Najeriya, kotun da in ta yi maka ko ba dai-dai ba, sai dai ALLAH ya isar maka da isarsa! Zata cigaba da sauraren kararar da bangaren Gwamnatin jahar Zamfara, su ka shigar akan cewa tabbas hukucin da wata babbar kotun Shari’a ta jahar Zamfara cewa jam’iyar APC ta yi zaben fitar da gwani Wanda ya cilastawa hukumar zabe karbar yan takararsu gaskiya ne. Hukucin da kotun daukaka Kara da ke zamanta a Sokoto ta jingine. Hukucin dai shi ne ya hana baiwa ‘yan takarar APC da na ‘yan Majalisar jaha da Gwamna da mataimakin da su ka lashe zabe, shedar lashe zaben.

Wannan shi ne zama na biyu Wanda za a yi gobe alhamis 16-5-2019. Duk da ba a tsammanin yanke hukuncin a ranar kuma a gun. Sai dai zaman zai zama kusan shi ne kashin Bayan Shari’ar domin zama na uku ana tunanen shi ne na yanke hukunci.

Hakaki wannan shari’a Tana da tasiri ga dukkanin al’ummar jahar Zamfara. Da dama na son a soke damar da aka baiwa ‘yan takarar APC. Wasu kuma na son a tabbatar da halaccin zaben Wanda zai baiwa dan takarar da ya lashe zaben Mukthar Shehu Idris. Zama Gwamnan jahar Zamfara. Ya Dora daga Inda mai gidansa Gwamna Abdul’azizu Abubakar Yari, ya sanya aya.

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment