Wata sabuwa wanda yafi kowa kokari a jarabawar share bagen shiga jami’a JAMB bazai samu shiga jami’a ba

Wani yaro dan shekaru 15 da haihuwa mai suna Ekele Franklin, ba zai samu damar shiga jami’a a wannan shekara ba, duk kuwa da cewa shi ya fi kowa samun sakamakon Jarabawar Shiga Jami’a mai kyau a kasar nan.

jiya ne dai Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’a (JAMB), ta fitar da sakamakon jarabawar, inda Franklin dan asalin Jihar Imo ya samu maki 347.
Wannan ne ya sa ya zama zakaran da ya fi kowa samun yawan maki, daga cikin mutane sama da 1,700,000 da suka rubuta jarabawar a cikin watan Afrilu da ya gabata.
Yaron dai ya rubuta a cikin fom din sa cewa Jami’ar Lagos ya ke so ta dauke shi.
Sai dai kuma shi da iyayen sa duk murna ta koma ciki, domin Shugaban Hukumar JAMB, Ishaq Oloyede, ya bayyana cewa zai yi wahala yaron ya samu shiga jami’a a bana, saboda karancin shekaru, wato shekarar sa 15 kacal.

Wani mai suna Emmanuel Chidebube ne ya zo na biyu, inda ya samu maki 346. Shekarar sa 16 kuma shi ma daga jihar Abia ya ke. Sai kuma na uku mai shekaru 17, mai suna Isaac Olamide daga Jihar Osun, ya samu maki 345.

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment