Wai suka ce haramun ne a ce “Ramadhan Kareen”!

A kowace shekara -a baya bayan nan- sai ka ga ana yada wata fatawa wadda kai da ganin ta, ka san so kawai ake yi a ta kura gami da rikici tsakanin al’umma..!!!

Cewa suke yi wai: haramun ne ka taya dan uwan ka murna da kalmar “RAMADHAN KAREEM”! Suna masu kafa hujja da cewa wai “ALKAREEM” sunan ALLAH ne, saboda shi ne yake bayarwa, shi kuwa RAMADHAN babu abin da yake bayarwa balle har ya zama “KAREEM”!

Lallai karamin sani ququmi..!! domin wannan kalma ta KAREEM a harshen Larabci tana zuwa da ma’anar wanda aka girmama, bayan ma’anar ta na mai karamci,, su a jahilcinsu sun taba ganin mutumin da yake ganin cewa watan RAMADHAN wani mutum ne da ya shaqe aljihunsa da kudi yana bi layi -layi, lungu -lungu yana bai wa mutane?!!

Babu shakka ma’anar KAREEM da ake danganta wa RAMADHAN ba ta wuce bayyana irin baiwa da karamci da Allah ya yi wa watan a tsakanin sauran watanni ba.., da ma ba domin wannan falala da karamci da Allah ya yi wa watan ba, da mai bai wajabta Azumi a cikin sa ba, kuma Musulmai suka kiran wannan wata da KAREEM ne kaman irin yanda Allah Madaukakin Sarki ya ba mu labari cewa: lokacin da wasikar Annabi Sulaiman (AlaiHis Salam) ya isa zuwa ga Sarauniya Bilqis, yana mai kiranta zuwa ga Tauhidi cewa ta yi:

((قالت يا أيها الملأ إني ألقي إلي كتاب كريم..)) (النمل: 29)

Ma’ana: ((Ta ce: ya ku mashawarta na an fa kawo mini wata wasika “Kareem” mai girma)).. Ma’ana dai a cikin wannan wasikar akwai wani abu mai girma wanda shi ne kadaita Allah Madaukakin Sarki, haka ma watan RAMADHAN, wata ne da yake da girma kwarai saboda Allah ya girmama shi, ba wai ana nufin shi ne mai bayar da girma ba..

Ban san mene masu yada wannan wasan yaran za su ce a Hadisin da Imamul Bukhari ya ruwaito da Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa Alihi wa sallam) yake yi wa Annabi Yusuf (AlaiHis Salam) kirari da cewa:

“الكريم بن الكريم بن الكريم بن الكريم، يوسف بن يعقوب بن إسحاق بن إبراهيم عليهم السلام”
ba?

Ma’anar: “Mai girma dan mai girma dan mai girma dan mai girma, Yusuf dan Ya’akub dan Is’haq dan Ibrahim (Alaihimus salam)”
Shin su a ganinsu kowanne daga cikin wadannan manyan mutane ya shaqe aljihunsa da kudi ne yana rarraba wa mutane, shi ya sa ya cancanci wannan kirari na ALKAREEM, ko kuwa ma’anar ita ce Allah Madaukakin Sarki ya girmama kowanne daga cikin su ya kuma karrama shi, wanda hakan ne kuma ya sanya suka cancanci a yi masu kirari ?!

A takaice dai, fadin RAMADHAN KAREEM ya halatta, su kuwa masu haramta fadin RAMADHAN KAREEM ” mai yiwuwa Allah ne yake son ya nuna wa al’umma hakikanin su a ilimi..

Saboda haka:

RAMADHAN KAREEM…

Sheik Saleh Kaura

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment