Yadda masana shari’a suke hangen yadda zata kaya a kotun koli ta nageriya wajen hukuncin shari’ar APC Zamfara.

MASANA SHARI’A SUNYI HANGE DA TSOKACI AKAN ABUBUWAN DA KOTUN KOLI ZATAYI AMFANI DASU A MAHANGAR ILIMI, DOMIN GUDANAR DA SHARI,AR APC JAHAR ZAMFARA.

Mafiyawan Masana Shari’a na hasashen cewa za’a gudanar da akalla zama biyu akan wannan matsala. A kotun ta koli dake garin Abuja Wanda za’a fara zaman a ranar 16th May 2019.


Zama na farko: za’a gudanar da muhawarori na aminta da rashin aminta na wasu bangarori na hukuncin kotun daukaka kara ta Sokoto (Brief of argument)

Zama na biyu: gabatar da hukunci, wanda daga gareshi sai dai kuma shari’ar dake gaban kowa ta Ubangiji inda acan za’a sake warware zare da abawa. (Waman ya’amal miskala zarratan khairan yarah, waman ya amal miskalan zarratan shairan…..)

A karkashin wannan an tanadi Takardun da zasu karfafawa wannan jayayya na aminta ko rashin aminta da sassan hukucin daukaka kara ta Sokoto wanda suka hada da:

1. Court order mai dauke da cewa Marafa da Yari faction to maintain status quo, kada kowane faction ya gudanar da wani abu na matsayin APC State party Excos. Wadda wata kotu a Abuja ta bada Umurni a wancan lokaci.

2. Lauyoyin Sen. Marafa sun gabatar da hujjoji na shari’a cewa kotun da aka faro shari’ar a Gusau bata da hurumin sauraren karar a mahanga ta shari’a.

3. Akwai report na mutane 7 commitee da Uwar Jamiyya ta tura suyi primaries wanda Dr. Abubakar Fari ya jagoranta, dake nuna cewa basu gudanar da zaben primaries duba da matsalolin da suka bijiro.

4. Haka kuma akwai report na committee na biyu wanda General Gana ya jagoranta wanda ke nuna cewar basu gudanar da primaries ba.

5. Akwai report na daga Hukumar INEC reshen jahar Zamfara wanda shugabar hukumar ta aikewa INEC ta kasa da cewa committees guda biyu da APC ta kasa ta turo basu gudanar da primaries a zamfara ba.

6. Akwai takardar da Chairman na APC ta kasa Adams Oshomole ya rubutawa Hukumar INEC cewa ba’a gudanar da Direct or Indirect Primaries a Zamfara ba, amma anyi consensus a City king Hotel Gusau.

Akan wadannan matsaloli ne hukumar INEC ta kasa ta tsaya tsayin daka cewa ba’a gudanar da primaries a Zamfara ba tun a wancan lokaci.

6. Acikin takardun hukuncin da kotun daukaka kara ta Sokoto ta bayar, ta bayyana cewa Zamfara High court bata yi bitar shedun da aka gabatar mata a gabanta ba (wanda suka hada da wasu da na zayyano a sama) yadda ya kamata kamin bayar da hukunci. Don haka ta jingene wannan hukunci nata

7. Akwai sheda a rubuce da kuma a faifan video dake nuna yadda bangaren gwamnati suka gudanar da zaben, inda wasu daga cikin turawan zaben nasu ‘yan takara ne kuma a lokaci guda.

DUKA WADANNAN ABABE MAFI YAWANCINSU AKWAI SU A TAKARDA AKWAISU KUMA A FAYAFAYIN BIDIYO DOMIN INGANTA SHEDA.

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment