Dole ‘Yan Nageriya su shiryawa juyin mulki-Balarabe Musa

Domin kusan kowa barawo ne

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Alhaji Balarabe Musa ya ce yanayin shugabanci a Najeriya ya cika shika-shikan juyin mulki ta fuskar lalacewarsa kamar yadda ya faru a Sudan kwanakin baya ko kuma sojoji su amshe mulki kamar na Venezuela idan dai abubuwa suka cigaba da dagulewa.


Tsohon gwamnan ya fadi haka ne a wata tattaunawa da ya yi da jaridar Vanguard kwanakin baya, inda ya ce lamura a kullum kara lalacewa suke yi.

Alhaji Balarabe Musa ya bayyana cewa ba a taba gudanar da zabe mafi muni a Najeriya ba fiye da na 2019.

A cewarsa ko a shekarar 1950 a lokacin da aka fara siyasa a Najeriya ba a yi amfani da kudi ba wajen jan ra’ayin jama’a ba. Wanda wannan kudin ne ya janye ra’ayoyin mutane.

A yanzu muna da shugabanni wadanda suke barayi ne, wanda ya shafi kusan kowa a Najeriya in banda rukunu biyu.

Rukunin farko su ne wadanda ba su sami damar yin satar ba, a yayin da rukuni na biyu su ne wadanda suka gwammace su mutu da su yi sata.

Wadannan rukunai na al’umma fa su ne suke wanzuwa a Najeriya, to ta yaya za a sami canji.

Ya kara da cewa saboda wasu rashin ingancin zabe da ake yi su ne musabbabin rashin tsaron da ake fama da shi a yanzu.

Duk da cewa wani minista a Najeriya ya zargi sarakunan gargajiya da hannu a matsalar tsaro. To wasu matakai gwamnatin tarayya ta dauka don maganin abun? Wannan gwamnatin babu wani abu da take yi wajen magance matsalar tsaro a Najeriya, banda karawa ‘yan ta’adda karfi da samun gindin zama.

Kuma a cewarsa lallai idan ‘yan ta’adda suka sami gindin zama sai batun juyin mulki kamar yadda ya faru a Sudan da Venezuela.

Su kuma malaman addini da suke cewa Allah zai kawo mafita. Amma kafin ka yi addu’a ya zama wajibi ka tsarkake niyyarka.

Wai ta yaya ne ma barawo zai roki Allah? Bayan mafi yawancin shugabanninmu barayi ne.

Balarabe Musa ya kawo misali da yadda kasashe irin su Iraki da Libya da Sudan da Venezuela yadda ba su a cikin kwanciyar hankali wanda nan gaba kadan Najeriya za ta bi sawunsu. A cewarsa ma na Najeriya sai ya fi lalacewa kasancewar a Najeriya ne ake sayen kuri’u kamar yadda ake sayar gyada a kan titi.

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

One thought on “Dole ‘Yan Nageriya su shiryawa juyin mulki-Balarabe Musa

  1. Duk hujjojin da wannan tsohon GWAMNAN ya bayar duk soki burutsu be, ta Yaya zaije kowa barawo ne, kuma shima Yana neman shugaban cin, na cin amana tunda shima barawon, sannan Don me yake ma kasar nan mugun roko na Shiga haula’i, Allah ya wadaran wannan Zancen naka na rashin son ci gaba.

    Like

Leave a comment