A sanarwa da ‘Yan gudun hijira da masaukai

A bisa ma’aunin Ilimi da hangen nesa, duk wanda ya baro garinsu, inda komai nasa a ce yake, kamar ‘yan Uwansa da abokansa, mahaifansa, wadanda suke a raye da kuma wadanda Allah yayi rasuwa, kuma ya baro abincinsa wanda zaici, ya baro dabbobinsa wadanda ya dogara da su, Kacokan! ya fantsama yayi kaura zuwa wani waje, inda shima kansa bai san inda ya maida gaba ba, ina ganin wannan shine mafi munin tashin hankali da firgici da ɗimauta.

A kullum a duk inda ka duba zakaga ‘yan gudun Hijira ne birgik a saman tituna suna yawon barace-barace cikin kaskance da takaici, musamman yara ‘yan Dagwai-dagwai wasunsu ma basu dade da fara iya tafiya ba, suna neman a taimake su, da abinda zasu ci, wasu daga cikinsu ko takalmin sakawa basu da haka nan suke yawo a Kasa cikin tagaiyara da nadama.

Haka idon mukayi la’akari da yadda idon mutun ya saba da wajen zamansa akace ya tashi yabar wurin ba tare da kintsawa ba, yaya yake ji a cikin ransa? A ‘yan baya-bayan nan shekaru biyu cikin na uku da suka gabata, a lokacin da Gwamnatin jihar Zamfara ta dingi tayar da mutane da sunan sun tare hanya a saman wasu daga cikin titunan Gusau, duk wadanda wannan lamari ya shafa, shin kokasan irin raɗaɗin da sunka ji?


Haka a lokacin da gwamnatin ta Jihar Zamfara ta dingi biyar Tashoshin Mota tana tayarwa da sunan Samar da tsaro a cikin al’umma, ina ganin kamar duk wanda wannan lamari ya shafa baiji daɗi ba, kasancewar akwai dubban jama’a da suke ciyar da iyalansu da ‘yan uwansu a ciki, wasu basu da inda suka dogara koma bayan hada-hadar da suke yi a wajen. Dukkanin wanda lamarin ya shafa a wancen lokacin bazaka iya auna irin bakin cikin da ya shiga ba.

Inko haka ne! To ina ga waɗanda hare-haren ‘yan Bindiga yasa su arcewa daga garuruwansu zuwa inda basu ma sani ba?

A daidai wannan gabar. Misali; A jihar Borno akwai kungoyin sa kai masu zaman kansu, waɗanda ba mallakar gwamnati ba munga yaddda suke kokari matuka ainun, wajen fafutukar samarwa da al’ummar yankinsu mafita, ta hanyar kokarin nemo tallafi na musamman ga wasu manyan kungiyoyin bada agajin gaggawa na duniya, kuma sunka basu haɗin kai da kwarin gwiwar hada karfi-da-karfe don kawo musu dauki ga al’ummarsu.

A Jihar Borno akwai wurare na musamman da gwamnatin Borno karkashin Jagorancin Gwamna Kashin Shattima ta ware domin kula da ‘yan Gudun Hijira. Duk kauyen da tashin hankali ya shafa suna iya zuwa wannan wuri da aka ware dominsu su zauna, su cigaba da da samun tallafi da kulawa da addu’ar samun zaman lafiya a cikin garuruwansu. Duk wanda yake da bukatar bayar da taimako zai iya zuwa wajen domin bayar da taimakon.

Amma mu jihar Zamfara har yanzu ‘yan gudun Hijiranmu sun kasa samun irin wannan gata cikin jama’a, ya kamata asan suma fa Mutane ne kamar kowa, sannan suma suna bukatar jin daɗin rayuwa kamar kowa, haka suma ba’ason ransu haka ya faru da su ba, tsautsayi ne wanda baya wuce ranarsa.

Inko haka ne! to meyasa baza’a taimakesu ba? Me yasa baza’a janyo
Su a jiki ba? Ko shakka babu irin kudaden da gwamnatin jihar Zamfara take kashewa duk wunin Allah wajen fannin siyasa da anyi amfani da koda rabinsu, wajen tallafawa ‘yan gudun Hijira tabbas za suji dadi, matuƙa duk da damuwar da suke ciki.

Kasancewsr yanzu azumi yana ƙarasowa shin ina makomar waɗannan bayin Allah? Tayaya zasu samu abinda za suci domin samun damar gabatar da ibada cikin sukuni da walwala? Haƙiƙa ya kamata a dubi ‘yan gudun hijira da idon rahama a taimaka musu.

Muna kira da babbar murya ga gwamnatin jihar Zamfara da ta dubi girman Allah ta taimaki ‘yan gudun hijira da wajen zaman na musamman wato ”Came” domin samu su tsugunna har Allah ya kawo musu ɗauki a maimakon raɓe-raɓen da suke yi a makarantu ana korarsa. Muna fata hadi da addu’ar Samun dauwamammen Zaman lafiya a cikin jihar Zamfara, da Arewa da Najeriya dama duniyar Musulmai baki daya.

Ya Allah ka karo mana arziki mayinwaci a cikin kasar nan.

Daga Nura Muhammad Mai Apple Gusau, dan Kungiyar Muryar Talaka ta Kasa Reshen Jihar Zamfara, kuma mai rajin Kare hakkin Dan Adam a Najeriya. Human Rights Defenders and Advocacy 08133376020

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment