RUNDUNAR SOJA TA KADDAMAR DA RUNDUNAR HARBIN KUNAMA A JAHAR ZAMFARA.

Rundunar soja ta kaddamar da RUNDUNAR harbin kunama a jahar Zamfara

RUNDUNAR SOJA TA KADDAMAR DA RUNDUNAR HARBIN KUNAMA A JAHAR ZAMFARA.

Shugaban Sojojin Nijeriya ,Mejojanar Yusuf Burtai ya kaddamar da Rundunar Harbin kunama kashi na uku da zasu tun kari dazuzukan jihar Zamfara, Katsina da Sokoto dan fafatawa da maharan da su ka addabin jahohin.


Mejoranar Lamidi Adewosun ya wakilinci Shugaban Sojojin a wajan kaddamar da Rundunar a Gusau baban birnin jihar Zamfara. Mejojanar Burutai ya bayyana cewa ‘ Rundunar Sojojin Kasarnan ta shirya Rundunar Harbin kunama dan tun karara mahara da su garkuwa da mutane da ke cin Karen su babu babaka a Dazuzukan jahohin Zamfara, Katsina da Sokoto.babu shakka Rundunar Harbin kunama zata tsaya tsayin daka dan ganin ta dakile yunkurin mahara da suka addabi yankunan.

Mejojanar Yusif ya mika godiyarsa da Shugaban kasa a kan gagarumar gudunmuwar da ya ke ba harkar tsaro da kuma karfafasu wajan ganin sun samu nasara a cigaba da yaki da ‘yan ta’ada.

Kuma a karshe shugaban Sojojn na kasa Mejojanar Yusuf Burtai ya tabbatar da cewa ‘ duk kayan aikin da Rundunar Harbin kunama kashi na uku ke bukata dan samun nasara aikin su zamu basu.

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment