Akuya ta zama magjiyar gari 

A karo na farko a tarihin kasar Amurka an zabi wata akuya mai suna “Lincoln” a matsayin magajiyar garin “Fair Haven” da ke yankin Vermont. 

A cewar kafar yada labarai ta Associated Press (AP ),an zabi akuyar a matsayin magajiyar gari ta musamman a garin “Fair Haven” wanda al’umarsa ta haura kimanin mutum dubu 2,500.

“Lincoln” za ta rike wannan mukamin a tsawon shekaru biyu tare da jagorantar da muhimman aiyuka da bukukuwan garin.

A cewar bayanan da shugaban garin “Fair Haven”, Joe Gunter yayi a wani taron manema labarai, an dauki matakin zabar akuyar a matsayin magajiyar gari saboda an share lokacin mai tsawo ba tare wani ya rike wannan mukamin ba.

Gunter ya kara da cewa, kimanin dabbobin 16 ne suka tsaya a takarar zaben magajin garin da aka shirya a garin nasu,inda kowace dabba ta biya dalar Amurka $5 don gwada sa’arta.

“Lincoln” mai shekaru 3 da haihuwa ce ta lashe wannan zaben ta hanyar samun kuri’u 13 a cikin 53 da aka jefa.

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment