IDAN BA’A SOKE ZABEN ZAMFARA BA, ZAI KAWO RIGIMA ◾◾◾◾◾ IN JI JAM’IYYUN ADAWA 

IDAN BA A, SOKE ZABEN ZAMFARA BA, ZAI KAWO RIGIMA▪▪▪JAMIYYUN ADAWA

Jam’iyyuka adawa da ke jihar Zamfara, sun tabbatar da cewa idan hukumar zaben ta kasa ba ta rushe zaben da ya gudana a makon da ya wuce na Shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya wan da ke cike da magudi, lalllai za a yi rigima.

Shugaban hadakar jam’iyyun adawa, dan takarar Gwamna a jam’iyyar Apga Alhaji Sani Abdullahi Wamban Shinkafi ne ya tabbatar da haka a dakin taron Wakilan kafafen yada labarai da ke Fadama a Gusau Baban birnin jihar Zamfara.

Shugaban hadakar ya bayyana cewa suna da tabbacin tun a ranar jajiberin zaben ne aka shirya wannan makircin yin magudi a hedikwatar ‘yan sanda da ke jihar, da Kwamishinan ‘yan sanda ya jagoranta Celestine Okoye da Kwamishiniyar zabe ta jihar Dakta Asamau mai Kudi da Shugaban jam’iyyar APC na jihar Zamfara, Honarabul Lawali Gamdon Kaura da Sakatarensa Honarabul Sani Mono kuma na je hedikwatar a lokacin aka hana ni Shiga a she akwai makircin da suke kullawa, a nan ne na nemi ganin kwamishinan, sai ya turo mini mataimakinsa a kan in fada masa abin da ke tafe da ni ni kuma na tsaya kai da fata na ce shi nake son gani.

Shi ya sa ya fito ya saurare ni kuma na tabbatar masa da cewa “Ba mu yarda da canza kayan zabe ba da Kwamishiniyar ke son yi, nan dai na fada masa korafin amma babu wani mataki da ya dauka.

Haka kuma runfunan zabe an saci akwatina, an yi amfani da mazabun ‘yan gudun hijira da Naira dari biyar da dubu daya don a zabi ‘yan takara gwamnati da kudin gwamnati. Kuma an kama mutane dumu-dumu sun kulle daki suna dangwale kuri’u kuma babu matakin daga Hukumar zabe da jami’an tsaro wannan ya tabbatar da cewa kitsa wannan makircin aka yi don haka mu jam’iyyu adawa ba za mu lamuncin wannan ta’addancin ba.

A kan huka muke kira ga Sufeto janar na ‘yansand da ya gaggauta dauke Kwamishinansa daga jihar Zamfara da ita kuma Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa da ta kori Kwamishiniyar zaben jihar don ba ta cancanci wannan aikin ba.

Wamban Shinkafin a madadin Shugaban jam’iyyun adawa sun dau alwashi bin umarni da Shugaban kasa ya bada na ganin bayan duk wanda ya saci akwati ko ya nemi kawo magudin zabe a jihar Zamfara, a zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jiha mai zuwa.

Gamayyar jam’iyyun sun hada da Jam’iyyar PDP, APGA,NRM ,ADC,YP ,ACCORD, ABP, da sauransu.

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment