Kanun labarun duniya 17-01-2019.

回 KANUN LABARUN DUNIYA 17-1-2019 回

◈ Buhari zai kaddamar da fara aikin tashar jirgin ruwa na farko a Arewacin Najeriya ranar Asabar.

Hukumar INEC ta saki sunayen ‘yan takara a jihar Rivers amma babu jam’iyyar APC a ciki.

Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya gana da wasu gwamnonin jihohi a fadar Aso Rock sun tattauna kan batun karin albashi.

Wata jaridar yanar gizo ta bayyana cewa ta samu labarin Atiku na shirin zuwa Amurka, gobe Jumma’a.

Shugaban Cibiyar Zaman Lafiya tsakanin addinai, Bishop Sunday Onuoha ya yi gargadin akwai yiwuwar Boko Haram zai watsu zuwa wasu jihohin Arewa.

Uwargidan Dr Bukola Saraki, Toyin Saraki taja Kunne akan mafi yawan masu neman wata kujerar mulki a Najeriya sun gaza,duk da zagewarsu. 

Jami’an tsaro su na cigaba da shiryawa zaben 2019 babu kaukautawa domin maganin magudi da rikici

Atiku Abubakar ya sha alwashin sayar da hukumar NNPC tare da rage ma’aikatan gwamnati idan ya zama shugaban kasa.

‘Yan Bindiga sun kai hari a anguwan Mayo-Gwai da ke Jalingo jihar Taraba, suka kashe mutane 3.

Gwamna Ganduje na jihar Kano ya dauki nauyin malamai mata guda 100 a jihar domin karo ilmi a Saudiyya.

Kotu ta bayar da umurnin amshe abun da ya yi saura na Naira bilyan 2 da rabi daga hannun babban hafsan soji, Amosun.

‘Yan Boko Haram sun kai wani hari a garin Gajiram da ke jihar Borno.

Gwamnatin tarayya ta bayar da umurnin rufe asusun ajiya na shugaban Alkalai na kasa, Onnoghen.

Hukumar NNPC ta samu N2.304trn daga cinkin albarkatun man fetir a cikin wata daya kacal.

Kungiyar kwadago ta kaddamar da yajin aiki a jahar Oyo zabe na saura kwanaki 30.

Kungiyar Daliban Najeriya ta ce ‘ya’yanta ba za su yi zabe ba muddin gwamnatin tarayya ba ta yi sulhu da ASUU ba kafin babban zaben 2019.

Jagoran kamfen din Buhari ya sauya sheka tare da wasu 5,000 a Akwa Ibom.

Atiku ya ce zai canja gwamnan CBN sannan ya bude bakin aljihun babban bankin kasa da gwamnatin APC ta tsuke.

Tsohon Ministan Harkokin Cikin Gida, Abba Moro ya ce wahalhalun rayuwa ne canjin da APC ta kawo wa ‘yan Najeriya.

Rundunar Yansandan Najeriya ta kama wani mutum da laifin kokarin kashe kansa a Lagos.

Tsohon Sufeto janar na ‘yansanda, Ibrahim Idris ya jadadda cewa ya yi iya bakin kokarinsa a lokacin da yake rike da kambun shugabancin hukumar.

Kungiyar MURIC ta roki kungiyar ASUU da su taimaka su duba halin da ake ciki su dawo aiki.

EFCC ta gayyaci Fani-Kayode da Odumakin kan labarin karya da suka saki na cewa jami’anta sun kai mamaya gida Alkalin-alkalai.

Majalisar dattijai a jiya Laraba, ta gudanar da zaman makoki a zauren majalisar wanda ya dauki tsawon mintuna 25 bisa rasuwar dan majalisar wakilai.

Wasu hadiman Gwamna Dankwambo na jihar Gombe sun sauya sheka daga PDP zuwa APC.

Mataimakin shugaban kasa ya nuna bacin ransa kan labarin gurfanar da Alkalin Alkalan Najeriya, inda ya ce Buhari ba shi da labari.

Hukumar INEC ta tantance sunayen da ke rajistan ta, ta cire sunayen wadanda shekarunsu bai kai 18 ba domin gudanar da zabe mai inganci.

Jam’iyyar APC za ta hukunta Okorocha da Amosun bisa zargin yi wa jam’iyya zagon kasa.

Garba Shehu ya ce yin batanci ga gwamnati ko rashin kunya ga shugaban kasa Buhari, ba zai zama adawa ta siyasa ba.

Yan bindiga sun kai ma jami’an hukumar kula da shige da fice hari a Katsina, sun babbaka ofisoshinsu da dakunansu.

Kotu ta kwace tikitin takarar dan majalisa daga hannun hadimin shugaba Buhari, Sha’aban Sharada.

Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Dakta Vincent Isegbe a matsayin shugaban sabuwar hukumar NAQS.

Tsohon Sufeta Janar na ‘yan sanda ya yi bukin cika shekaru 60 a duniya a ranar da ya yi murabus daga aiki.

An binne gawar mutane 26 da ‘yan bindiga suka kashe gandi a karamar hukumar Rabah da ke Sokoto.

Ganduje ya kaddamar da cibiyar raba wutar lantarki ta N500m a karamar hukumar Doguwa ta jihar Kano.

Gwamna Geidam na jihar Yobe ya umarci asibitocin jihar da su yi wa masu ciwon koda ‘yan asalin jihar aiki kyauta.

Kasashen Turai da Amurka na shirin baiwa hukumar ‘yansanda kariya gabanin zaben 2019.

Mutane 3 ne suka jikkata sakamakon fashewar wani abu a garin Lyon na Farasa.

Dutsen Shindake da ke Tsibirin Kuchinoerabu a kasar Japan ya fara aman wuta.

Amurka ta kama wata ‘yar jaridar Press TV mallakar Iran.

Kungiyar IS ta dauki alhakin harin da ya hallaka mutane 15 da suka hada da jami’an sojin Amurka 3 a Syria

A jihar Oromiya da ke kasar Ethiopia wasu mutane dauke da makamai sun aikata fashi a bankuna 18.

Adadin mutanen da suka mutu sakamakon harin ta’addanci da aka kai a Nairobi Babban Birnin Kasar Kenya sun kai mutum 15.

Wani rahoto ya ce dubannin ‘yan gudun hijra a sansaninsu na Rann suka tsallake zuwa Kasar Kamaru.

Mutum 1 ya rasa ransa inda sakamakon wani harin ta’addanci da aka kai da bam a Kabul Babban Birnin Afganistan.

Kungiyar Tarayyar Afirka za ta tattauna matsalolin ‘yan gudun hijira.◈

╰→ 📧 Jekadiyarzamfara@gmail.com

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment