Kanun labarun duniya na yau 14-1-219.

KANUN LABARUN YAU 1412019

◈ Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta kama wasu mutane 4 a jihar Legas, wadanda take zargin suna sayen Shanun sata daga ‘yan bindigar da ke kai hare-hare a jihar Zamfara

An harbe mutane biyu har lahira, wasu da dama sun samu raunuka yayin wani rikici da ya barke tsakanin magoya bayan APC da PDP a Ilorin.

Gwamnonin yankin Kudu maso kudancin Najeriya sun gana kan al’amarin gurfanar da Alkalin alkalai, Walter Onnoghen, kasancewan dan yankin ne.

Rundunar sojoji sun kwance manyan bamabamai da ‘yan Boko Haram suka binne.

Ka daina yi wa Buhari sharri – Fadar shugaban kasa ta gargadi gwamna Ortom.

Atiku ya ja kunnen Obiano akan ya daina yiwa shugaba Buhari kamfen domin a cewarsa hakan ya saba ra’ayin yan Igbo.

Wata babbar mota makare da shinkafar kamfen din APC ta kashe mutane 45 a jihar Ekiti.

Jigo a jam’iyyar PDP kuma na kusa da Sule Lamido, Baba Santali ya koma APC.

Ambasada Musa Ibeto ya jagoranci wasu ‘yan jam’iyyar PDP suka koma APC a jihar Neja.

‘Yan Boko Haram sun kai farmaki a garin Magumeri da ke jihar Borno.

An nada, Alhaji Musa Isah Mustapha Agwai a matsayin sabon Sarkin Lafia.

Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Katsina ta sanar da samun nasarar kama wasu mutane biyu da sukayi garkuwa da wata tsohuwa a karamar hukumar Safana. 

Yaki da ta’addanci: Tsohon shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida mai ritaya ya jinjina ma Dakarun Sojojin Najeriya.

Tsohon gwamnan jihar Niger, Babangida Aliyu, ya ce shugaban kasa Buhari zai fadi takara a zaben 2019.

Garken Kudan Zuma sun tarwatsa mutanen kauyen Gunsun da ke karamar hukumar Kanam a jihar Filato.

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu ya gargadi gwamnatin tarayya a kan hadarin da ke tattare da gurfanar da alkalin alkalai, Walter Onnoghen a gaban kotu.

Dan takarar gwamna na APC a Kwara ya sha da kyar yayin da ‘yan daba suka tarwatsa kamfen dinsa a Ilorin.

Hukumar yan sanda ta mayar da Melaye zuwa hedkwatar SARS bayan ya ki shiga asibitin DSS.

Alkalin kotun hukunta ma’aikatan gwamnati wato CCT, Jastis Danladi Umar, ya sanar da daga gurfanar babban alkalin Najeriya zuwa rananTalata, 22 ga watan Junairu, 2019.

Secondus ya ce APC da Buhari sun fara ne da kawo rudani a tsakanin ‘yan siyasa da yan majalisun tarayya inda har aka yi yunkurin juyin mulki.

Makiyaya sun sheke wani mai sana’ar su har lahira tare da raunata wasu Masuntan biyu a jihar Delta.

Alhaji Atiku Abubakar, ya ce PDP zata dauki duk wasu matakai da ya dace don dakile jam’iyya mai mulki ta APC daga tafka magudi a zabe mai zuwa.

An ci gaba da cecekuce gami da barin baya da kura kan lamarin haramta fatauci da ta’ammali da barasa a jihar Kano.

Rundunar soji, a ranar Lahadi ta ce ta gano hanyoyin da mayakan Boko Haram ke samun kayayyakin da suke amfani da.

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PPC ya sha alwashin cin galaba akan Buhari da Atiku a zaben 2019.

Rotimi Amaechi ya ce, jam’iyyar PDP na fama da fatara da yunwa kuma tana son dawowa gwamnati ne domin sake tafka sata.

Wani babban fasto na jihar Osun, Seun Adeoye, ya ce tsanani a Najeriya ba zai yanke ba muddin aka sake zaben Buhari a watan gobe.

An kama wata mota makare da bindigogi da alburusai a jihar Ogun.

Gawurattaun Lauyoyi 150 da za su tsayawa Onnoghen a Kotu ba tare da an biya su ba.

Da alamu Sanata Ekwerenadu yayi watsi da yakin neman zaben Atiku Abubakar.

‘Yan takarar gwamna hudu na jam’iyyar PDP sun dunguma sun koma APC a jihar Neja.

Yuguda ya tuno yadda suka hana shugaban kasa Buhari wajen da zai kaddamar da yakin zabensa a Bauchi, a 2015.

Atiku Abubakar ya cacaki gwamnatin Shugaba Buhari game da shirinta na sakin tubabbun ‘yan Boko Haram. 

Rundunar ‘Yan Sanda Ta Kama Wata Mota Makare Da Alburusai Guda Dubu 34,865, Inda Ake Shirin Shiga Da Su Jihar Anambara Daga Jamhuriyyar Benin.

Mutum 15 Sun Rasu A Iran Bayan Jirgin Soji Ya Tarwatse.

Kungiyar Taliban ta kashe ‘yansanda 4 a Afghanistan.

Tarzomar karin farashin biredi ya yi sanadiyar mutuwar mutane 24 a Sudan.

Sakamakon munin yanayi da yake damun kasar Egypt an dakatar da ayyuka a tashoshin jiragen ruwa 5 da ke kasar.

Wani jirgin saman dakon kaya ya fado a yankin Sefadesht da ke karkashin lardin tehran Babban Birnin Kasar Iran.

Ivanka Trump na neman zama shugaban Babban Bankin Duniya.

Matasan Falasɗinu sun mayar da martani ta hanyar jifa da duwatsu da kuma kone taya.

Rukunin farko na sojin Amurka sun fara ficewa daga Syria.

Wata gobara da ta tashi a tsakiyar Paris ta raunata mutane 12.

Majalisar dokokin Macedonia ta rattaba hannu kan a wani sabon kudurin sauya sunan kasar zuwa “Jamhuriyar Arewacin Macedonia”. ◈

📧 Jekadiyarzamfara@gmail.com

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment