An kama manyan ‘yan kasuwa dake daukar nauyin ‘yan bindiga a jahar Zamfara. 

AN KAMA MANYAN ‘YAN KASUWA DAKE DAUKAR NAUYIN ‘YAN BINDINGA A JAHAR ZAMFARA.

‘Yan sanda sun kama wasu mahauta ‘yan asalin jihar Zamfara mazauna Legas bisa zarginsu da daukan nauyin ‘yan bindigar Zamfara.

Mahautan guda hudu da aka kama sune 

(1) Alhaji Ago Atine

(2) Alawani Abubakar

(3) Mohammad Sahagari

(4) Bashir Aliyu. 

Alhaji Altine ya ce wani Alhaji Naira ne ke sayar masa da shanun da araha shi kuma ya sayar da su da tsada a Legas

Sashin tattara bayanan sirri na ‘yan sanda ya gano cewar ‘yan bindigan na amfani da kudin da suke samu daga sayar da shanun satar ne wurin sayo makamai Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kama wasu mahauta hudu da ke sayar da nama a Agege na jihar Legas bisa zarginsa da daukan nauyin ‘yan bindiga da ke kai hare-hare a wasu garuruwa a jihar Zamfara.

The Punch ta ruwaito cewa garuruwan da aka kai harin sun hada da kananan hukumomin Tsafe, Zurmi, Shinkafi, Maradun, Mari da Birnin Magaji.

‘Yan sandan sunyi ikirarin wadanda ake zargin su ke samarwa ‘yan bindigan kudaden da sukae sayan makamai ta hanyar sayan shanun sata daga hannunsu.

Wadanda ake zargin sune Alhaji Ago Atine, Alawani Abubakar, Mohammad Sahagari da Bashir Aliyu. Legas: 

An kama manyan ‘yan kasuwa dake daukar nauyin ‘yan bindigar Zamfara: An gano cewar ‘yan bindigan da suka kashe mutane da dama sunyi amfani da kudin da suka samu bayan sayar da shanun ne wajen sayo bindigu da wasu muggan makamai daga kasar Libya. 

Majiyar Legit.ng ta gano cewa sashin tattara bayyanan sirri na ‘yan sandan Najeriya sun damke kwamandan ‘yan bindigan ne a Zurmi kuma ya tona yadda ‘yan bindigan ke samun kudin sayan makamai.

An kama wadanda ake zargin su hudu ne yayin da suke kokarin sayar da wasu daga cikin shanun satar ga wani mutum. Daya daga cikin wanda ake zargin, Alhaji Altine ya shaidawa City Round cewa ya saya shanu fiye da 400 daga wani Alhaji Naira. Sai dai ya ce bai san cewa shanun sata bane.

Ya ce, “Alhaji Naira ya aiko min da shanu fiye da 400 ni kuma na sayar masa a mayanka. Na tura kudin zuwa asusun ajiyar bankin Alhaji Naira. Na saya shanun da araha, ya sayar min da kowanne guda a kan N60,000 zuwa N70,000 ni kuma na sayar da kowanne a kan N170,000 zuwa N180,000. Ban san abinda Alhaji ya ke yi da kudin ba kuma ban san shanun na sata bane.”

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment