KANUN LABARUN DUNIYA NA YAU 10-1-2019.

KANUN LABARUN YAU 1012019

Gwamnatin Jihar Zamfara tana cigaba da gano wasu masu rike da sarautun gargajiya da ke taimakawa ‘yan ta’adda a jihar.

Hukumar NDLEA A Kano Ta Kama Masana’antar Sarrafa Magungunan Jabu.

Sakataren Jam’iyyar PDP Ya Canza Sheka Zuwa APC A Kebbi.

Gwamnan Da Ya Fifita Rayuwar Al’umma A Kan Nashi Zai Iya Biyan Albashin Naira 30,000 –Shugaban NLC Na Kano. 

NAFDAC Ta Kwace Kayan Kwalliyan Mata Na Jabu Na Naira Miliyan 60 A Legas. 

NEXIM Ta Ware Naira Biliyan 36 Don Bukasa Jihohin Arewa.

Kayan Da Ake Shigowa Da Su Nijeriya Sun Lashe Naira Biliyan 837 A Watanni 11.

Cutar Kwalara Da Zazzabin Lassa Ta Kashe Mutum 993 A Nijeriya A 2018.

‘Yan Fashi Sun Farmaki Shugaban Kungiyar Kwadago Na Jihar Benuwai.

An Cafke Dan Shekara 25 Da Laifin Satar Mota A Neja.

Saboda Buhari aka samu rangwamin tsanani a Arewa maso Gabas inji Gwamnan Imo, Rochas Okorocha.

‘Yan Shi’a sun nemi Amurka ta sanya baki domin gwamnatin Najeriya ta sako Sheikh Ibrahim El-Zakzaky.

Buhari ya amince da gina sabbin jami’o’i 4 a fadin Najeriya.

Zaben 2019: Ba zan yadda a fiddo kudin gwamnati a yi yakin neman zabe ba – Buhari.

Tsohon shugaba PDP, Adamu Muazu ya koma APC.

Atiku Abubakar ya yi alkawarin bai wa matasa da mata ayyukan yi idan ya sami nasara.

Farfesa Wole Soyinka ya ce dan Najeriya ne zai kirkira tare tare da yada labarin bogi da zai jawo yakin duniya III.

Babbar Kotun tarayya za ta fara sauraron karar haramtawa shugaba Buhari takara a zaben 2019.

Kungiyar kwadago za ta kauracewa zaben 2019 kan rashin tabbatar da sabon mafi karancin albashin ma’aikata.

Sojoji sun kwato manyan bindigu 45 daga hannun ‘yan ta’adda a jihohin Nasarawa da Taraba da Benue.

An kammala wasu sabbin tashoshin lantarki 8 da biliyoyin kudi.

PDP ta nemi Tinubu yayi watsi da Buhari ya bi Atiku domin a gyara kasa.

‘Yan bindiga sun kashe mutane 4 a wani hari da suka kai kauyen ‘yar Santa da ke karamar hukumar Kankara na jihar Katsina. 

Sakataren PDP na jihar Kebbi, Alhaji Muhammadu Sakaba ya sauya sheka zuwa APC.

Hukumar Sojin Najeriya ta karyata rahotannin da ke cewa ta kulle babban hanyar Maiduguri zuwa Damaturu a ranan Laraba.

Mataimakin shugban kasa ya ce labaran karya ya nemi ya kunna wutar rikici tsakaninsa da matarsa.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce zai zabtare albashin dukkanin wani ma’aikaci da ke daukar sama da mafi karancin albashi a kasar.

‘Yan sanda sun bazama neman wanda ya tayar da tarzoma a yayin kaddamar da kamfen din APC a Legas.

Karamar ministar harkokin waje, Hajiya Khadija Bukar Ibrahim ta yi muraus daga kan kujerarta.

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya kaddamar da cibiyar zaurukan sada zumunta ta a garin Abuja.

Shugaba Buhari ya ce ‘yan sandan Najeriya sun gaza sauke nauyin da ya rataya a wuyansu da hakan ya sanya dakarun soji ke kai komo a tsakankanin al’umma.

Kungiyar Buhari ta yi zargin cewa Ekweremadu da wasu gwamnonin PDP na yi wa shugaba Buhari aiki don ganin ya lashe zabe mai zuwa.

Gwamnatin Kano zata mayar da yin gwajin kwayoyi farilla ga duk wanda za a bawa mukamin siyasa.

Wasu masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da kansilar Majan Wayya dake karamar hukumar Charanchi.

Shugaba Buhari ya ce ba zai yiwu a bai wa ‘yan sanda makamai ba kuma wasu gwamnonin su gaza biyan su albashi.

Uwargidan gwamna Bagudu ta fara yiwa Buhari kamfen din gida-gida a Kebbi 

Sabon tsarin zabe, INEC ta ce ana tantancewa ana jefa kuri’a.

Sanata Shehu Sani ya taya yayan kungiyar kwadago, NLC, zanga zangar tabbatar da karin sabon tsarin karancin albashi na N30,000.

Jirgin kasan Kaduna-Abuja ya samar da N960,000,000 ga gwamnatin Najeriya.

Buhari ya ce ya yiwa yan Igbo adalci duk da bai samu kuri’u da yawa daga gare su ba a zaben da ya gabata.

An fara samun nasara wajen hana iyaye aurar da kananan mata a jihar Neja.

Ministan yada labarai, Lai Muhammad ya ce gwamnatin tarayya ba ta da nufin hana yada labarai.

Wani Lauya ya gargadi Buhari kan tsawaita wa’adin Sufeto Janar na ‘yan sanda. Ya ce ka da ya kuskura ya yiwa kudin tsarin mukin kasa karan tsaye.

Yanzu kam an tabbatar Katsina na cikin matsala, musamman matan aure masu badala da codeine.

Sakatare Janar na Kungiyar Kwadago ta Indiya Amarjeet Kaur ya bayyana cewa, kusan ma’aikata miliyan 200 sun tsunduma yajin aiki kwanaki 2.

‘Yan sanda 13 ne suka mutu sakamakon harin da kungiyar ta’adda ta Taliban ta kai kan wani caji ofis dake gundumar Chaharbulak a jihar Belh dake Afganistan.

Jamus ta ce ta gano an kama daya daga cikin ‘yan kasarta 2 da suka bata a Masar.

Falasadin ta soki Isra’ila bisa shirin sake gina sabbin gidaje a Baytullahim.

Kasar Rwanda ta haramta samar da duk wani man shafawa ko sabulu mai sanya haske a kasar.

📧 Jekadiyarzamfara@gmail.com

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment