▩ KANUN LABARUN DUNIYA 10-11-2018 ▩
◈ INEC ta wallafa sunayen ƴan takara na jihar Zamfara, babu ɗan takara ko ɗaya daga jam’iyyar APC.
◈ Sarkin Gummi, Justice Lawal Hassan ya koka kan salon yaki da rashawa irin na gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.
◈ Gwamnatin Buhari ta gurfanar da tsohon Shugaban NDDC a gaban Kotu.
◈ Ana shirin fatattako wasu ɗaliban jihar Kano da ke karatu a waje.
◈ Uwar gidan shugaban kasa, Aisha Buhari ta mika lambar yabo ga wata mai shara a filin jirgin sama na Abuja.
◈ Kwamitin Shugaban ƙasa ba shi da ikon kwace kadarori – Kotun daukaka ƙara.
◈ Magoya bayan Atiku sun gargaɗi Ezekwesili da kakkausar murya.
◈ Ƴan sanda sun damke wani da ke yaudarar mutane da sunan Atiku a Facebook.
◈ Ibrahim Shekarau ya ce ƴan Kwankwasiyya za su yi da-na-sani bayan 2019.
◈ Ƴan sanda a Lagos sun kama wani matashi da caka wa abokinsa kwalba a ciki kan ₦400.
◈ Kotu ta bayar da belin ɗan sandan da ya harbe ƴar uwar tsohuwar ministan kuɗi.
◈ Hukumar tattara kudaɗen haraji, FIRS ta tara Naira tirilyan 4.3 daga watan Janairu zuwa Oktoba.
◈ Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II zai gina katafaren kamfanin sarrafa iskar gas a jihar Akwa Ibom kan kuɗi $1.1 bilyan.
◈ Majalisar Tarayya ta amince da ƙudirin cire ka’idojin shekarun mai neman aiki.
◈ Hukumar Kwastam ta damke kwantena cike kayan Sojoji da makamai a jihar Rivers.
◈ Ƴan baranda sun kwace majalisar dokokin jihar Ondo bayan tsige kakaki.
◈ Majalisa za ta soke N-Power idan ya koma siyasa a cewar Shehu Sani.
◈ Bukola Saraki ya ce lallai Atiku Abubakar zai lashe zaben 2019 da gagarumin rinjaye.
◈ Ƴan Boko Haram sun kashe mutane tara har da soja a jihar Borno.
◈ Fayose ya ce muddin Buhari ya zarce za a shiga cikin matsanancin yunwa a Najeriya.
◈ Majalisa ta nemi a kori shugaban hukumar NEMA saboda salwantar da Naira bilyan 33.
◈ Majalisar wakilai za ta binciki badaƙalar da jam’iyyu suka yi a zaben fid da gwani.
◈ Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta saki sunayen ƴan takarar gwamna 67 na zaben 2019.
◈ Dole Buhari ya saki Tiriliyan daya ga jami’o’in ƙasar nan kafin mu janye yajin aiki a cewar ASUU.
◈ Sowore ya ce Najeriya za tayi kuɗi da tabar wiwi idan ya zama Shugaban kasa.
◈ Mayakan Boko Haram sun kai ma matafiya harin kwantan bauna, sun kashe da dama a Borno.
◈ Ƴan Shi’a sun karyata Lai Mohammed kan cewa ana ciyar da shugabansu N3.5m duk wata.
◈ Shugaban ƙungiyar Boko Haram ya fitar da sabon bidiyo inda ya yi kaca-kaca da waɗanda su kace wai ya mutu.
◈ Sanata Dino Melaye ya yi hasashen cewa tsohuwar jam’iyyarsa ta APC za ta tarwatse nan ba da jimawa ba.
◈ Majalisar dokoki na jihar Ogun ta tsige kakakinta, Bamidele David Oloyelogun da mataimakinsa.
◈ Ku mutunta doka – Hukumar Birtaniya ga ƴan Shi’a da hukumomin tsaro.
◈ Lauyoyi 120 ne za su tsayawa mutanen da ake zargi da kashe manjo janar Alkali.
◈ Ƴan bindiga sun kai wani hari a Birnin Gwari na jihar Kaduna.
◈ Gwamnatin tarayya ta ce yawaitar matasan da ba su da aikin yi na matuƙar barazana ga tsaro da cigaban Najeriya.
◈ Gwamna Ifeanyi Okowa ya bukaci ƴan Najeriya su mayar da al’amurransu ga Allah saboda shi kaɗai ne zai iya warware matsalolinsu.
◈ Musulmai a jihar Filato sun bukaci a ba su mukamin mataimakin gwamna.
◈ Ƴan bindiga sun sace ɗan takarar sanata da shugaban jam’iyyar ADC na jihar Ondo.
◈ Ma’aikatan hukumar filin jirgin sama sun yi barazanar shiga yajin aiki.
◈ An gargaɗi masu aikin zabe da ka da su ce za su hana a saci akwatin zabe, in an fara su bar wurin.
◈ Da takaici, yadda Najeriya ta zama ta 2 wajen yin kashi a bainar jama’a inji Buhari.
◈ Kasar Amurka ta yi ammana da irin shirye-shiryen da INEC ke yi domin zaben 2019
◈ Gwamnonin 6 ne suka bayyana cewar za su iya biyan N30,000 ma fi karanci albashi.
◈ Atiku Abubakar ya kara wa dukkan ma’aikatansa albashi na mafi karancin albashi na Naira 33,000.
◈ Buhari ya kaddamar da dokar-ta-baci a kan tsafta da samar da ruwa a Najeriya.
◈ Mutane 3 sun mutu, 5 sun yi bace a wani hatsarin jirgin ruwa.
◈ Sowore ɗan takarar shugaban kasa ya ce zai kama IBB da Obasanjo idan ya samu nasara.
◈ An kamo bakwai daga 13 da suka saci ma’aikaciyar lafiya a kwanakin baya a Yola.
◈ Kungiyar ƙwadago ta sake yin barazanar tafiya yajin aiki idan har gwamnatin tarayya ta yi kokarin canja baki kan N30,000.
◈ Hukumar DSS ta yi wa shugaban jam’iyyar APC na kasa tambayoyi kan zaben fid da gwani na jam’iyyar.
◈ Ɗan bindiga daɗi ya hallaka mutane a wani gidan shakatawa da ke Amurka.
◈ Ministan harkokin shari’ar ƙasar Amurka Jeff Session ya yi murabus daga mukaminsa.
◈ Jam’iyyar Republican ta shugaban Amurka ta rasa rinjaye a Majalisar Wakilan Kasar bayan zaben tsakiyar wa’adi.
◈ An kashe dan majalisar Somaliya a wani harin bam a Mogadishu.
◈ Girgizar kasa mai karfin awo 5 da afku a kasar Ostireliya.
◈ Mahaukaciyar gobara na ci gaba da lakwame dazuzzuka da kuma rayukan al’umar Amurka.
◈ Shugaba Ali Bongo na Gabon ya farka daga doguwar suma da ya yi tun a watan Oktoba.
◈ Ebola na ci gaba da barna a Kongo.