▦KANU LABARUN DUNIYA 6/11/2018▦
◈ Shugaba Buhari ya gana da wasu jiga-jigan gwamnati da kuma malaman addini.
◈ Gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong ya bayyana cewar shugabanin al’umma da na addini ne suka ɗaurewa masu laifi gindi a jihar.
◈ Najeriya za ta cigaba da fitar da ganyen Zobo kasar Mexico.
◈ Majalisar dattawa ta kaddamar da bincike kan harin kisan da aka kai wa Ekweremadu.
◈ Yariman kasar Burtaniya, Charles da uwargidarsa sun iso Najeriya.
◈ Wasu sanatocin APC sun yi ganawar sirri da Shugaba Buhari a fadar gwamnatin tarayya.
◈ Kar ku raga wa masu furta kalaman batanci, ku cafke su – Buhari ga jami’an tsaro.
◈ Jam’iyyar APC mai mulki ta rasa wasu mambobinta guda huɗu a majalisar wakilai zuwa wasu jam’iyyun siyasa.
◈ Gwamnatin tarayya ta ce ba ta da isassun kuɗaɗen da za ta biya wa kungiyar ASUU bukatunsu.
◈ Majalisa ta ɗage takunkumin kin tantancen naɗe-naɗen shugaba Muhammadu Buhari.
◈ Daga gidan yari! Dariye ya jadadda goyon bayansa ga Buhari da Lalong a zabe mai zuwa.
◈ Yadda sojoji da ƴan sanda suka kashe ƴan Shi’a 492, rashin adalci ne a cewar Falana.
◈ Gwamnatin Najeriya ta karyata raɗe-raɗin canza Ministan kuɗi.
◈ Gamayyar ƙungiyoyin kwadago na kasa sun janye yajin aikin da suka tsara shiga a yau.
◈ Ministan kuɗi Zainab Ahmad ta rantsar da sababbin kwashinonin kotun daukaka kara na haraji.
◈ Ministan ilimi, Adamu Adamu ya roki Malaman jami’o’i da su janye yajin aikin da suke yi don a cigaba da tattaunawa.
◈ Gwamnan jihar Filato, Lalong ya roki Buratai ya yafewa al’ummar jiharsa na kisan Janar Idris Alkali.
◈ Gwamnati na ciyar da ƴan makaranta da kwai miliyan 6m da shanu 594 duk mako.
◈ Sojoji 149 ne ke fuskantar hukunci kan amfani da kafafen yada labarai na zamani ba bisa ka’ida ba.
◈ Hukumar INEC ta cire sunayen mutane 300,000 daga rijistar masu zabe.
◈ A jiya Litini manyan Malaman kasar Saudiyya suka ziyarci hedikwatan ƙungiyar Izala na kasa.
◈ Shugaban majalisar dattawa, Saraki ya karbi ƴaƴan jam’iyyar APC 5,000 da suka koma PDP a Kwara.
◈ Mutane biyu sun mutu sakamakon karyewar wata gada a garin Hanti-Mansiysk na kasar Rasha.
◈ Hukumar Bincike Kan Kayan Tarihi ta Indiya ta hana a yi Sallah a Masallacin Taj Mahal mai dimbin tarihi.
◈ Ɗalibai a Japan na kashe kansu saboda damuwa da ke damunsu.
◈ An rantsar da shugaba Paul Biya a wa’adi na bakwai a Kamaru.