KANUN LABARUN DUNIYA 5/11/2018
◈ Majalisa ta gano wata badakalar kuɗi a NNPC da ka iya janyo a tsige shugaba Muhammadu Buhari.
◈ Kungiyar ASUU ta ce babu ruwanta da duk wani alkawari da gwamnati za ta sake dauka domin an sha su sun warke.
◈ Jam’iyyar APC ta yi kira ga a binciki ziyarar da Atiku ya kai Dubai.
◈ Rahoton da babban bankin Najeriya ya wallafa ya nuna cewar kuɗaɗen da kasar ke samu daga man fetur na raguwa.
◈ Kungiyar Shi’a ta saki jerin sunayen mambobinta 34 da Sojoji suka kashe.
◈ INEC ta haramtawa jami’anta shiga kungiyoyin WhatsApp(groups).
◈ Gwamnan jihar Filato ya je yi wa Buratai ta’aziyyar kisan Manjo Janar Idris Alkali a yau.
◈ Peter Obi ya kai wa Sanata Rabiu Kwankwaso ziyara a Abuja
◈ Atiku ya kalubalanci Buhari kan kyautar Dala 500,000 da ya bai wa Guinea Bissau.
◈ Gwamnonin APC za su hadu da sanatocin jam’iyyar don tsige Oshimhole.
◈ Za a buɗe katafren kamfanin sarrafa tumatur a jihar Katsina.
◈ Yan JTF sun yi nasarar kashe ƴan Boko Haram da dama a karamar hukumar Gubio jihar Borno.
◈ Ƙungiyar malaman jami’o’i, ASUU ta shiga yajin aiki sai Baba-ta-gani a yau.
◈ Ƙungiyar SERAP ta bukaci Buhari ya sanya baki a harkallan bidiyon Ganduje.
◈ Rundunar ƴansanda a jihar Filato ta nuna mutane 19 da ake zargi da kisan Manjo Janar Idris Alkali.
◈ An kasa samun matsaya tsakanin gwamnati da kungiyoyin ƙwadago.
◈ Yarima Charles na Ingila zai kawo ziyara Najeriya a makon nan inda zai gana da Buhari kan tsaro.