YADDA ZAKA NEMI AIKIN NPOWER CIKIN SAUKI

YADDA ZAKA NEMI AIKIN NPOWER CIKIN SAUKI

ABUBUWAN DA AKE BUKATA. 

1.Mafi karancin kwalin da ake bukata a wannan bangaren shi ne kwalin sakandire (SSCE result).

2. Asusun Banki (Bank Account)

3. BVN Ka tabbata sunan da zaka yi amfani da shi ya yi daidai da wanda yake cikin BVN dinka, haka zalika shekarun haihuwa.

4. Kanann Hotuna (Passpot)

5. ID card ( Voters’ card ko National Id card)

6. Za a shiga http://www.npower.gov.ng ko kuma npvn.npower.gov.ng domin cike takardar neman wannan aikin (Application Form)

Kamar yadda sanarwa ta gabata makon da ya gabata cewa gwamnatin tarayya zata dauki sababbin ma’ikata na Npower, to a wannan karan za a koyar da sana’o’i ne wanda suka hada da;

  1. AUTOMOBILE: Wannan bangaren ya shafi koyar da hanyoyin gyaran mota na zamani ta hanyar amfani da na’ura mai kwakwalwa wanda ya hada; OBD scanner da wheel balancing da kuma panel beating.

 2. Agriculture Equipment Technicians (Agric Tech) : Shi kuma ya shafi yadda za a sarrafa Motoci da injuna da ake amfani da su wurin noma, da kuma yadda ake kula da su.

3. CARPENTRY & JOINERY : A nan kuma za a koyar da aikin kafinta, musamman na bangaren aikin gini, ma’ana kafintan Sama.

4. ELECTRICAL INSTALLATION: wannan bangaren kuma yana kunshe da fannin wayarin na wuta da kuma gyaran wuta. 

5. MASONRY & TILING : Shi kuma wannan za a koyar da aikin gini ne da kuma yadda ake saka tayil da falasta da kuma dabe.

6. PLUMBING & PIPEFITTING : A wannan bangaren kuma za a koyar da abin da ya shafi yadda ake yin wayarin din ruwa da kuma yaddaa ake hada hitar wanka ta zamani da yadda ake shirya fayif -fayif na ruwa.

7. HOSPITALITY: Shi kuma wannan aji ya kunshi yadda ake hada kayan kwalam da makulashe kamar su kyak(cake) da kuma gike-girke na zamani. Wannan kusan shi ne yake da alaka da mata kai tsaye.

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment