ƘUNGIYAR NAN MAI YIWA AL’UMMA HIDIMA TA LABOUR ROOM GLOBAL INITIATIVES TA KARRAMA ƘUNGIYAR MATASA ‘YAN GWAGGWARMAYA DA CERTIFICATE. 

ƘUNGIYAR NAN MAI YIWA ALUMMA HIDIMA TA LABOUR ROOM GLOBAL INITIATIVES TA KARRAMA ƘUNGIYAR MATASAYAN GWAGGWARMAYA DA CERTIFICATE

DAGA: Nura Muhammad Mai Apple Gusau

A bisa jajircewa da nuna bajinta. ƙungiyar Labour Room ta karrama ƙungiyar Matasa Ƴan Gwaggwarmaya masu fafutikar ganin an samu sauyi mai ma’ana a cikin al’umma, domin kara zaburarwa ga resu, don ganin sun ƙara ƙaini wajan ayukansu na yau da kullum. kowa ya san ƙungiyar Matasa ‘yan Gwaggwarmaya ƙungiya ce wanda ta tsayu da kanta kuma babban burin wannan kungiya shine ta shahara a Duniya wajan aiki tuƙuru ga ƴan Ƙasa.

Ƙungiyar matasa ƴan gwaggwarmaya ba ƙungiya bace wanda anka buɗe da manufar siyasa, ko goyon bayan wani, ko wasu, ”a a” manufar ta shine ganin an samu jagoranci abun alfahari wanda kowa yake cike burin ganin an sama.

Da wannan muke miƙa saƙon godiya ta musamman ga Ƙungiyar Labour Room da fatan Allah ya kara daukaka, Allah kuma ya ci gaba da zaunar damu Lafiya a jihar Zamfara da Ƙasa baki Ɗaya.

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment