MUNAFUNCI DODO YAKANCI MAISHI 

MUNAFUNCI DODO YAKANCI MAISHI

Daga; Amag Abdoul 

Dama tin tashin farko mun fada maku cewa wlh gajere bai cancanci jagorancin jahar Zamfara ba Amma a wancan lokacin wasu Dan kawai salon maula da kin gaskiya sukaci gaba da kariyar Gwamnan hayaniya Kuma jagoran gidan Yarin Kiri-kiri a 2019 Insha Allah.

Gwamnan hayaniya bai taba zaunawa cikin jahar sa ba don kariyar rayukan Al-umma ba sai gashi ya zauna cikin jaha don kawai ya samu ya tsayar da dan takarar da Zai rufa Masa asiri daga ta’asar da yayiwa jahar Zamfara a cikin shelarun mulkin sa.

Wani babban abun kunyar shine Gwamnan hayaniya duk bai gaji da rayukan da aka salwantar ba a jahar sai gashi yayi biris da hukunci Jam’iyar sa wai Zai jagoranci zanga zanga.

Alhamdulillah munyi zanga zanga Kuma munce “adaina kashe mu” Kuma an zage mu duk mun dauka Kuma Allah cikin ikonsa bayan zanga zangar mu da wasu Dan lokuta kiranmu ya karbo.Yau me zaku Kira Gwamnan hayaniya dashi ?

To kasani yakai Gwamnan hayaniya komai zakayi sai kabar mulkin nan,Kuma maganar Dora Wanda Zai rufa maka asiri wannan karya Kuma zanga zanga kaje kayi dakai da yan Koren ka makiya talakawa Amma kashirya jagorantar wadannan mukarraban naka zuwa gidan Yarin Kiri-kiri bayan ka ajiye mulki.

Fatanmu anan Allah ya zaba Mana shugabanni na gari ba irin wadannan jagororin hayaniyar ba.

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment