SHIN APC NA IYA HADE KAN ‘YA’YANTA BAYAN FIDDA ‘YAN TAKARA? 

Shin APC na iya hade kan ‘ya’yanta bayan fidda ‘yan takara?

Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya za ta yi zaben fitar da ‘yan takara na gwamnonin jihohin Bauchi da Legas da Zamfara wadanda aka dage zuwa yau litinin. 

Dukkanin jahohin guda uku na fama da rikicin cikin gida na jam’iyyar APC tsakanin masu hamayyar neman kujerar gwamna.

A jihar Bauchi ‘yan jam’iyyar za su sake fitowa ne domin zaben fidda gwani bayan da zaben ya ci tura a ranar Lahadi.

Uwar jam’iyyar ta kasa ce ta dage zaben, bayan da wakilanta da za su yi zaben suka kasa isa jihar a kan lokaci.

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment