IDAN MILIYOYIN TALAKAWA ZA SU KAWAR DA BAMBANCE-BAMBANCE DA KE TSAKANINSU DOMIN MARA MAKU BAYA, TO YA ZAMA WAJIBI KU 8 KU YI HAKA!

IDAN MILIYOYIN TALAKAWA ZA SU KAWAR DA BAMBANCE-BAMBANCE DA KE TSAKANINSU DOMIN MARA MAKU BAYA, TO YA ZAMA WAJIBI KU 8 KU YI HAKA!

Daga: Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau

Hakika Duk wanda ya ga yadda talakawan jahar zamfara, muka dunkule waje daya, wasunmu daga jam’iyu daban-daban da ma bangaren ‘yan Takara 8 na APC. Kowa ya kawar da ra’ayinsa da dalilin da ya sa yake biyar wanda ya ke biya, ya aminta da cewa: zai karbi daya daga cikin ku ‘yan Takarar 8 da kuka aminta ya yi maku Takarar gwamna a jam’iyar APC.

Kuma duk wannan ya faru NE, sanadiyar Gwaggarmayar da yanzu talakawan su ke yi, na kawar da Wanda gwamnan jahar Zamfara ya bayyana yana goyawa baya a zaben gwamnan jahar Zamfara a Fitar da gwani dama babban zaben 2019.

To tabbas za mu ga cewa Duk abunda ya koro bera ya fada wuta to ko shakka babu yafi wutar zafi.

Wanda mu a tunanenmu tuni kun tsayar da Wanda ya cancanci ku Marawa baya, kamar yadda ya zama dole ku yi.

Abunda ya faru jiya, da dare, ya tarwatsa zuciyar mafi yawanmu. Domin yadda jam’iyar APC matakin jahar Zamfara, ta fito ta ci karenta babu babbaka ta hanyar yin kutunguilar da za ta kassara guiwar talakawa wajen fitowa zaben fitar da gwani na gwamna wanda shi ne mai zafi. Sai dai babban abunda ya ke kwantar muna da hankali, shi ne; yadda uwar jam’iyar APC ta Kasa ta haramtawa jam’iyar APC ta Jahar Zamfara tsoma bakinta a cikin zaben YAR-TIKE na gwamna da ke jahar.

Sai dai wani hanzari ba gudu ba, hakika maganar marafa na kan hanya, ta cewa ita kanta uwar jam’iyar APC ba ta shirya yin adalci a zaben YAR-TIKE din da ta ce za ta yi ba. Domin yau Assabar 29-9-2018 amma har yanzu ba a turo, jami’an da za su Kula da zaben a gobe Lahadi 30-9-2018 ba. Kuma in sun zo wajen gwamnatin jaha, za su yi, haka zalika ita ce, za ta ba su ma’aikatan da za su yi aiki da su. Hakan na nufin anki cin biri anci dila kenan!

Dan kamar yadda Sanata Marafa ya fada mafi a’ala shi ne, dukkan ‘yan Takarar 8 ku kauracewa shiga zaben har sai uwar jam’iyar APC ta shirya yin zaben Kuma kamar yadda ta ce ita zata shirya shi Dari-bisa-dari, to Sai hakan ta kasance tukun.

Wanda duk aka yi haka, to da ikon Allah nasara na ga hannun talakawan Zamfara, domin mun shirya kuma mun yi alkawarin ba za a yi muna doki Dora ba. Za mu nemi yancinmu da aka taushe tsawon lokaci.

Dan haka muna amfani da wannan damar mu yi kira ga sauran ‘yan takara biyar da su ma su kauracewa shiga wannan zaben har sai an tabbatar da an shirya, yin zaben cikin adalci.

Ita kuwa uwar jam’iyar APC ya kamata ta tashi tsaye daga mummunan barcin da ta ke yi, akasin hakan to hakika mu talakawan jahar za mu dawo daga rakkiyar jam’iyar, domin dama mu mutun mu ka saba zabe, domin kakaba muna wanda ba mu so zai iya sa mu sauya sheka domin zaben wanda zai jagorance mu kan turba ta gari.

Da haka muna Kira ga wadannan yan Takarar da su sani cewa wallahi mu talakawa Allah muka dogara da shi, ku muka dogara da ku, Dan haka dole ku cigaba da kawar da duk wani BAMBANCE-BAMBANCE ku rungumi juna domin ceto mu. Domin dai wallahi muna neman ceton ku, Wanda kuma hadin kai dai zai sa ayi nasara domin hausawa na cewa Taron yawa yafi Taron karfi.

Allah ya sa mu dace amin.

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment