Sabon Rikicin 2019: A Na Zargin Yarima Da Shirya Wa Wakkala Gadar Zare A Zamfara. 

Sabon Rikicin 2019: A Na Zargin Yarima Da Shirya Wa Wakkala Gadar Zare A Zamfara

Daga shafin leadership Ayau 

Siyasar jihar Zamfara karkashin jagorancin jam’iyar APC mai mulkin jihar na neman canza salo a sakamakon tsayar da dan takara da gwamnatin jihar ta yi a karkashin jagorancin shugabannin jam’iyar ta APC, wanda ta bayyana cewa, dan takararsu na gwamna shi ne Hon Mukhtar Shehu Idris, watau Kogunan Gusau kuma kwamishinan kudi na jihar, wanda Gwamna Abdula’ziz Yari ne ya tabbatar da haka jin kadan bayan kammala taro na masu ruwa da tsaki a harkar jam’iyar ta jihar ga manema labarai a gidan gwamnati jihar da ke Gusau.
Wannan sanarwar ta girgiza ’yan takara masu neman tsayawa kujerar gwamnan, musamman mataimakin gwamna, Malam Ibrahim Wakkala Liman, lamarin da a ke gani tamkar wani hadin baki ne a tsakanin shi gwamnan da tsohon gwamnan jihar, Ahmad Sani Yariman Bakura. Sai dai Gwamna Yari ya kara da cewa, “wannan ba zai hana duk mai ra’ayin sayen fom din takara ba ya saya, amma mu kam ga dan takararmu.
” Majiya mai tushe ta bayyana wa LEADERSHIP A YAU LAHADI cewa, masu iya magana na cewa ‘mai zufin ido da wuri ya ke fara kuka. Wannan ya sa Mataimakin Gwamna Malam Ibrahim Wakkala Laman ya garzaya gidan uban siyasar jihar Zamfara kuma jigo a jam’iyyar APC, Sanata Ahmad Rufai Sani Yariman Bakura a kan matakin da gwamnati ta dauka kuma a matsayinsa na limamin canji, wanda duk abinda Gwamna Yari zai yi sai ya nemi shawararsa ko ya san da haka, kuma an kira wasu ’yan takarar a Abuja da sasantawa da su, amma shi ba a kira shi ba.
Sai Sanata Yarima ya bayyana cewa, shi bai san da haka ba, kuma shi da kansa zai raka Malam Ibrahim Wakkala ofishin jam’iya na kasa ya sawo fom kuma shi zai bada kudin fom din. Wannan ne ya sanyaya wa Malam Wakkala zuciyarsa da tunanin cewa, hakarsa za ta cimma ruwa. Ranar Litinnin da ta gabata ne tawagar Malam Wakkala su ka garzaya Abuja don sayen fom tare da jigonsa kuma garkuwarsa Sanata Yariman Bakura, amma kafin isarsu gidan sai a ka ce mu su lallai Sanata Yarima ba ya nan kuma ba a san inda ya ke ba, wato kamar ya yi batan dabo kenan. Wannan ne ya sa Malam Wakkala ya fahimci cewa, akwai lauje a cikin nadi, saboda ba haka su ka yi da mai gidan nasa ba.Wannan ya sa ya fidda kudi daga aljihunsa ya tunkari ofishin jam’iyyar ya sawo fom dinsa da kansa.
A ranar Talata kuwa sai magoya bayansa su ka yi ayari zuwa bakin iyakar Zamfara da Katsina, don tarbo dan takararsu, Malam Wakkala Liman, inda ya shigo da dubun-dubatar mutane a na ‘sai Wakkala ko da Yarima ba ya so’. Tawagar tasa ta kai ziyara gidan Sarkin Katsinan Gusau, Mai Martaba Ibrahim Bello, inda daga nan ta wuce gidansa, inda ya yi jawabin godiya ga magoya bayansa.
LEADERSHIP A YAU LAHADI ta tuntubi wani mai fashin baki a harkar siyasa a jihar Zamfara, Dakta Nasiru Gusau, wanda ya bayyana na ma ta cewa, “wannan shirin ba zai taba yiwu ba sai da Sanin Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura, saboda shi ne uban kuwa a cikin siyasar jihar Zamfara kuma babu mai iya sanin tsakaninsu da Gwamna Abdul’aziz Yari sai Allah. “Tare su ke yin duk abinda Gwamna Yari ya ke kullawa. Da shi a ke yi.
Idan ba da shi a ke yi ba, me ya sa bai yi magana ba tun da abin ya faru? Kuma me ya sa a lokacin da Mataimakin Gwamna Malam Ibarhim ya je sayen fom ya yi ma sa layar zana ko kasa ko sama su ka rasa inda ya ke? Kuma har yanzu babu wata magana da ta fito daga bakinsa na kin amicewarsa a kan abinda gwamnati ta yi na fidda dan takara!” Abin mamakin dai shi ne, sanin kowa ne cewa, duk fadin jihar Zamfara babu dan ga-ni-kashe-nin Sanata Yariman Bakura irin Malam Ibrahim Wakkala, don duk wanda ya taba yakar Yarimawa ko kuma ya kasance makiyin Sanata Yarima ne lallai ba sa taba shan inuwa daya da Malam Ibrahim Wakkala kuma duk wani taron da gwamnatin jiha ko jam’iyya za ta shirya, idan Sanata Yarima bai samu zuwa ba,sai Malam Wakkala ya kawo uzirinsa kuma ya nuna ya na tare da wannan taron da a ke yi, amma sai ga shi kuma a na neiman a gan su a rana wannan karon. Bincikenmu ya nuna cewa, tun bayan farauwar lamarin rikicin Yarima ya sulale ya bar kasar zuwa birnin London; lamarin da mafi yawan na hannun daman Wakkala ke kallo a matsayin wata dabara ce ta kauce wa dafa wa dan takarar nasu a shata dagar da ya yi da gwamnan jihar, Abdul’aziz Yari.

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment