DAN WASAN SUPER EAGLES ZAI YIMA SAKKWATAWA KYAUTA IDAN SUKACI KANO PILLARS.
Dan wasan bayan tawagar kwallon kafa ta Najeriya, Super Eagles, Shehu Abdullahi ya yi alkawarin bai wa kungiyar kwallon kafa ta Sokoto United kyautar kudi idan suka ci Kano Pillars.A wani sakon bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Abdullahi ya yi alkawarin bai wa kulob din na Sokoto naira 100,000 kan kowace kwallon da ya ci idan ya samu nasara a kan kungiyar Kano Pillars.