TARIHIN KISAN GILLA A ZAMFARA 2011/18

Tarihin Kisan Gilla A Zamfara. 2011-2018
Daga Abdulrashid Abdullah kano

A Farkon Shekarar 2012 Yan Bindiga Sun Kashe Wasu Yan Kasuwa Mutum 15 Kuma Suka Konasu Yayin Da Suke Dawowa Kasuwa Daga Kauyen Shamushalle.
Haka 12 Ga Watan Mayu, 2012, Yan Bindiga Sun Harbe Wasu Mutum 8, Yan Sanda 4 A Kauyen Dansadau, 11 Ga Watan Yuni Kuma Wasu Mahara Sama Da 80, Dauke Da Muggan Makamai Suka Dirarma Kauyukan Dan-Gulbi, Garu, Sabuwar Kasuwa, Da Biya Suka Hallaka Mutane Sama Da 26.
Aranar 30 Ga Watan October, An Kashe Sama Da Mutum 20, Harda Wani Dagaci A Kauyen Kabaro Dake Yankin Dansadau, 14 Ga Watan December, Yanbindiga Suka Bindige Wasu Yan Banga Mutum Goma A Kauyen Rukudawa Na Kamar Hukumar Zurmi.
18 Ga Watan Yuni Na Shekarar 2013, Yan Bindiga Sun Kai Hari, Kauyen Kizara Dake Gundumar Karamar Hukumar Tsafe, Inda Suka Hallaka Mutane Sama Da 48, Ciki Harda Wani Hakimi Da Limamin Kauyen Da Shugaban Yan Banga Na Yankin, Hakazalika Wani Rahoto Ya Tabbatar Da Cewa Yan Bindiga Sun Kashe Sama Da Mutum 160, Tareda Sace Matan Aure 10, A Watan July Na Wannan Shekarar
Haka Kuma An Kashe Wasu Mutum Uku A Kauyen Buzuzu Dake Yankin Bukuyum.
A Wannan Shekarar Dai Suka Dirarma Kauyukkan Yan-kuzo, Zamfarawar-Girke, Kofa, Kundubau, Wonaka, Furar-Girke, Fegin Mahe, Kukar Fandu, Kawana, Lafiya Da kauyen Gora, Suka Hallaka Mutane Sama Da 33 Tareda Arcewa Da Garken Shanu.
Awatan July Na 2015 Sun Sake Kashe Mutane Sama Da 30 Tareda Sace Shanu Masu Yawa A Kauyen Kokeya Da Chigama Na Yankin Binnin Magaji. Ranar 6 Ga Watan Fabrairu Na Shekarar 2016, Yan Bindiga Sun Kashe Sama Da Mutum 50 Tareda ‘Kona Gidaje A Wani Harin Tsakar Dare Da Suka Kai Kauyen Kwanar Dutse Na Yankin Maru.

hakazalika An Sake Kashe Wasu Masu Ha’kar Ma’adinai Kusan 40 A Kauyen Gidan Ardo Dake Gundumar Karamar Hukumar Mulki Ta Maru.

Hakazalika A Cikin Wannan Watan Aka Sace Mutane 40 Tareda Kora Shanu Da Dama Anan Maru, Wasu Mutum 25 Sun Sake Rasa Rayukkan Su A Kauyen Dole, Tudun Bugaje Da Kwangwami.

A Farko Farkon Wannan Shekarar Ne Ranar 14 Ga Watan Fabrairu, 2018, Aka Yima Wasu Kauyawa Kisan Gilla A Cikin Wata Motar Daukar Kaya, A Kauyen Birane. Haka Kuma A Cikin Wannan Shekarar Ne Aka Yima Hakimin Kauyen Kucheri Kisan Gilla.

A Cikin Dararen Goman Karshe Na Watan Ramadan Nan Daya Wuce Ne Wasu ‘Yan Bindiga Suka Lashe Mutum 31 A Hare-Haren Da Suka Kai Wasu Lauyukan Karamar Hukumar Birnin Magaji.

Inda Hare-Haren Suka Shafi Kauyuka Hudu Dake Cikin Yankin Kiyawa Da Gora A Karamar Hukumar Birnin Magaji.

An Kashe Mutane Sama Da 50 A Cikin Mako Daya A Zamfara, Inda Aka Kashe Mutum 23 A Kauyen Zaloka A Karamar Hukumar Anka Da Kuma Mutum 27 Da Aka Kashe A Yankin Gidan Goga Dake Karamar Hukumar Mulki Ta Maradun.

Wannan Tarihin Kisan Kiyashin Da Ake Yi Mana A Zamfara Kenan A Takaice, Shin Ina Zamfarawa Zamu Sa Kan Mu? 

Laifin Suwaye Gaza Dakile Wannan Matsala Tsawon Shekaru 7 Da Mahara Suka Dauka Suna Cin Karen Su Ba Babbaka?

Rahoto Ya Nuna Cewa Akwai Kauyukka A Jihar Zamfara Da Mazauna Kauyukkan Suka Samu Damar Sulhuntawa Da Mahara Akan Zasu Rinka Biyan Haraji Idan Har Suna Son Zaman Lafiya Da Samun Damar Noma A Gonakin Su.

Awasu Kauyukkan Kuma Yan Bindigar Sun Shaidama Mazaunan Wajen Cewa Sun Gaji Da Satar Shanu Yanzu Tsabar Kudi Suke So Akasa, Don Haka Kamin Su Shigo Kauye Da Mako Daya Zasu Aiko Da Takardar Cewa Rana Kaza Suna Tafe Don Haka Suna Son Ahada Masu Kudi Milyan Kaza..Dole Masu Tumakai, Shanu Da Buhuhuwan Hatsi Ayita Kaiwa Kasuwa Sai An Tattara Kudin Da Suka Buqata Sai Aba Mai Anguwa Ko Jakimi In Sun Zo Su Amsa…

Wai A Zamfara Dan Ta’adda Yanada Lasisin Kashe Rai, Daukar Lamuni Da Bada Wa’adin Lokaci Akan Buqatar Sa.

Allah Yasa Wannan Ya Zama Na Karshe.

Allah Ka Agaza Mana.

Allah Ka Zaunar Damu Lafiya.

Ameen!

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment