SALLAR IDI DA LAYYA, DAGA SHEAK ABDULHAKEEM AHMAD YA’AKUB GUSAU.

SALLAR IDI DA LAYYA 

Sheak Abdulhakeem Ahmad Ya’akub Gusau

Sallar Idi an shar’antata ne, Shekara ta Farko bayan Hijra

HUKUNCE HUKUNCEN TA

Sallar Idi Sunnah mai karfi, domin tun da aka farata, Annabi saw bai dainaba, har wafatinsa

A Babbar Sallah, ba’a cin abinci sai andawo ga mai LAYYA da Wanda bazaiyi ba

Ana son ayi wanka, ayi aswaki, ashafa turare, asaka sutura sabuwa in akwai (kala tafi) a tafi kasa

Ba’azayi aski ba, ko cire kumba, ga Wanda zai yi LAYYA, sai andawo

Za’a tafi Masallaci, cikin natsuwa ana Kabbarori har a isa, idan anje filin Idi

Za’a samu wuri a zauna a Kira Liman kuma ba’a yin Nafila koda Gaisuwar Masallaci

Idan Liman yazo, za’a gyara sahu, ba kiran Sallah ko Iqama, za’ayi Sallah raka’a biyu bayyane

A yayin Sallah, duk sanda za’ayi kabbara za’a daga hannuwa, bayan an Sallama, a saurari Khuduba

Idan Liman yagama Khuduba, yayi Addua, sai ya yanka Ragonsa, don Jama’a Susan ya yanka, idan sunje gida su yanka

Idan za’a dawo gida, za’a canza hanya, za’a dawo ana Kabbarori,

Ana taya juna Murnar Sallah

Zuwan Mata Idi ya halatta, koda masu Haila da Nifasi, SAI DAI, bazasuyi Sallar ba, zasuji Khuduba, su samu addu’a

An Halatta bukukuwan Sallah, matukar babu sa6on Allah ciki.

LAYYA DA HUKUNCEN HUKUNCEN TA

Ma’anarta:

Itace dabar da ake yankawa. ranar Sallah don Neman kusanci da Allah

Hukuncinta:

Sunnah ne wajiba akan duk Wanda yake da ikon yinta daga cikin Musulmi

Namiji ko Mace, Babba ko Yaro, Mazauni ko Matafiyi, banda Alhaji da yake Mina

Falalarta:

Sunnar Baban ku CE (Annabi) Ibrahim AS, kuma kowa ne gashi yanada lada(Hakim, Tirmizi)

Hikimarta:

*Neman kusanci da Allah, ta hanyar kama horon Sa

*Raya Sunnar Kakan Annabawa Ibrahim da koyi da Annabi saww

*Godewa Allah bisa Nimarsa hore mana dabbobi na daga cikinsu

*Yalwatawa Iyali da mabukatan ta hanyar raba Naman

Dabbobin da ake LAYYA dasu:

*Rago ko Tunkiya

*Bunsuru ko Akuya

*Sa ko Saniya

*Rakumi ko Rakuma

Shekarun Dabbobin:

Rago yakai Wata 8, Bunsuru Shekara, Shanuwa Shekaru 2, Rakumi Shekaru 5

Dabbobinda basu LAYYA:

Gurguwa, Mai karyayyen kaho, Wadda idonta ya mutu, Wadda kunnenta ko Wutsiya ya gutsire, marar lafiya, wadda batada kitse, ramamma, da sauransu

Rana da Lokacin Yanka:

Ranar Sallar, bayan sallar Idi kuma sai bayan Liman ya yanka

Wanda bai samu damar yiba, zai iya yankawa kwana 2, bayan Sallah, kuma ana yakan ne daga bullowar rana zuwa karkatawa

Wake yanka LAYYA?

Duk Wanda zaiyi LAYYA shi zai yanka dabbarsa ko mace CE, idan zata iya

Ya halatta yin wakilci, ga Wanda bazai iya ba, amma anso a yanka gabansa

Biyan Masu aiki/Sai da Fata:

Idan mutum yayi layya, bai halatta sayarda fata, ko biya mai yanka ko fida ko gashi da wani bangare na dabbar

Kamar fata ko wuya ko kai da kafafu da sauran su, amma za’a iya basu sadaka, bayan jingarsu

Layyar Hadaka/Hadin gwiwa: 

A Mazhar Malikiyya ba’a bada kudi asayi dabba ayi LAYYA, amma daya idan yayi zai iya shigarda ko mutane nawa sai shi tarayya a lada

Amma a Mazhabar Hanabila, ana iya bada kudi mutane 7, sukayi Shanuwa ko Rakumi su yanka, amma da Shekaru

Raba/Ajiye Naman LAYYA:

An so kasa naman gida 3, aci 1, ayi kyauta da1, ayi sadaka da 1.

Ya halatta ajiye naman LAYYA har wani lokaci, amma idan akwai Mabukata bai dace ba.

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment