GWAMNONIN JAHOHI TARA 9 MUSULMAI DA ZASU CI TALIYARSU TA KARSHE SUNA RIKE DA MUKAMIN GWAMNA.

GWAMNONIN JAHOHI TARA 9 MUSULMAI DA ZASU CI TALIYARSU TA KARSHE SUNA RIKE DA MUKAMIN GWAMNA. 

Yayin da ake ta shirye-shiryen bukin babbar sallah a satin nan mai kamawa wato ranar talata mai zuwa, wasu gwamnoni da dama a Nigeriya na shirin yin bikin sallarsu ta karshe ne a saman karagar mulki musamman ma idan akayi la’akari da cewaa zaben gama gari zai zo ne a farkon shekarar 2019.

Nuni ne da cewa bayan wannan sallar, karamar sallah da za ta zo idan muna da rai zata kasance ne a cikin watan juni na shekarar 2019 bayan an yi zabe har ma an rantsar da sabbin gwamnoni. 

Sunayen gwamnini musulmai da kuma suke kan wa’adin su na karshe gasu kamar haka:

1- AbdulAzizu Yari na Jihar Zamfara

2- Abdulfatah Ahmad na Jihar Kwara

3- Abiola Ajimobi na Jihar Oyo

4- Ibikunle Amosun na Jihar Ogun

5- Ibrahim Geidam na Jihar Yobe 

6- Ibrahim Hassan Dankwambi na Jihar Gombe


7- Kashim Shattima na Jihar Borno 

8- Tanko Almakura na Jihar Nasarawa 

9- Ogbeni Rauf Aregebesola na Jihar Osun.

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment