SOJOJI SUN KASHE WANI SHAHARARREN DAN TA’ADDA A ZAMFARA

SOJOJI SUN KASHE WANI SHAHARARREN DAN TA’ADDA A ZAMFARA. 

MAJIYA DAILY TRUST

Sojojin da suke yaki da ‘yan ta’adda a jahar zamfara sun kashe wani shahararreb dan ta’adda mai suna Sani Dan Buzuwa, da wasu ‘yan ta’addan biyar, awani hari da sojojib suka kai a gandun dajin kuyanbana dake a jahar ta, zamfara. 

Dayake bayyana ma manema labarai: mai magana dayawun ruduna ta daya ta Sojojin Nigeria Col Muhammad Dole, yace “An kashe wani Sojan Nigeria daya dakuma wasu biyu dasuka samu raunuka ayayin wannan artabun”. 

Haka rundunar Sojojin sun gabatar da wasu bindigogi da alburusai da sukace sun gano adajin lokacin aratabun makaman sun hada da bindiga mai kirar 1 x AK47 rifle, 3 x magazines, aburusai 87, masu Kirar 7.62mm dakuma babban makami namusamman mai kirar 1 x G3 rifle, 4 x magazines da aburusai 61, masu kirar 7.62mm (NATO).

Published by jekadiyarzamfara

Wannan shafi an bude shine domin sanar da ku halin da duniya take ciki tare da ilmantarwa da nishadantarwa. Ga masu sha'awar turo muna sakonninsu suna iya turo muna sakon Email; - Jekadiyarzamfara@gmail.com A tabbata ana da sahihancin labarin da za'a turo muna tare da shaidar hotuna ko video. Mun gode da kasancewa da jekadiyarzamfara

Leave a comment